Hotunan yajin aikin masu burodi a Kano

Masu sayar da burodi a jihar Kano sun yi yajin aikin kwanaki uku, saboda tashin farashin fulawa.

Kofar wani gidan burodi da ya shiga yajin aiki.
Bayanan hoto, Gidajen burodi kamar wannan sun shiga yajin aiki a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Ma'aikata ba su fito aiki ba
Bayanan hoto, kungiyar masu gidajen burodi ta shiga yajin aiki na kwanaki uku, domin nuna damuwa kan karin farashin kayayyakin hada burodin.
Hatta wajen gasa burodi na gargajiya ma a rufe yake
Bayanan hoto, Farashin fulawa wanda shi ne kan gaba a kayayyakin hada burodin ya tashi sosai.
Wani gidan burodi na zamani, amma ba a gasa burodin
Bayanan hoto, Masu gidajen burodin da ke yajin aiki sun danganta tsadar fulawa da tashin dala.
Wasu kayan gasa burodi
Bayanan hoto, A cewarsu farashin alkamar da ake shigo da ita Najeriya domin yin fulawar ne ya tashi.
Wani gidan burodi a Kano
Bayanan hoto, Inda a kan jera burodin bayan an gasa ya yi fayau a irin wadannan gidajen burodi.
Wani wajen sayar da burodi
Bayanan hoto, Rashin gasa burodin ya shafi masu sara su sayar.
Shagon wani dan tireda
Bayanan hoto, 'Yan kasuwa kamar wannan dan tiredan dole suka rufe shago.
kwallar wani mai shayi a kan murhun da ba a hura ba.
Bayanan hoto, Hatta Masu shayi ma kwallarsu ta yi hutun dole, saboda karancin burodi a jihar.
Wani teburin mai shafi ba kowa
Bayanan hoto, Yawancin gwagware a jihar sun koka yadda rashin burodin ya sa suka rasa abin kalaci.