SARS: Akwai masu ɓoyayyar manufa kan zanga-zangar EndSARS - Mai Mala Buni

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe
Bayanan hoto, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce akwai buƙatar shugabannin al'umma su sa baki wajen kawo karshen zanga-zangar #EndSARS.

A cewarta ɓata-gari na iya raɓewa da ita su tayar da hankali.

Shugaban Jam'iyyar na riko, Alhaji Mai Mala Buni, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Yobe, ya ce ci gaba da aka yi da zanga-zangar, alama ce da ke nuna cewa akwai masu ɓoyayyar manufa - bayan gwamnati ta saurari kukan matasan - kuma ya kamata a yi kaffa-kaffa da su.

Gwamna Buni ya sanar da haka ne a wata hira da yayi da wakilin BBC Ibrahim Isa.

Ya ce "Najeriya ƙasa ce da wasu ke da burin a sake fasalinta, inda wasu kuma ke da burin a raba ta."

Ya kuma ce akwai ɓata gari, wadanda a ganinsa su ne wannan rundunar ta EndSARS ke kokarin kawar wa.

Ya yi kira ga shugabanni a dukkan matakan mulki da su "dawo cikin hayyacinsu" saboda sai akwai ƙasar sannan za a zauna lafiya, sannan ne mutum zai iya cimma ko wane irin burin da yake da shi.

Bayanan sautiNIGERIA ENDSARS APC

Ku latsa alamar lasifika da ke jikin hoton Gwamna Buni domin jin cikakkiyar hirar da yayi da Ibrahim Isa na BBC Hausa.

Tashin-tashina tunzura mutane ke haifarwa

Gwamnan ya soki abin da ya kira tunzura mutane da wasu ke yi saboda dalilai na siyasa.

"Idan aka tuzura mutane bisa tituna kan wasu bukatu - ko na neman mulki ta bayan fage - ba abin da zai haifar illa tashin-tashina."

Ya jam'iyyar APC ke kallon wannan zanga-zangar?

Gwamnan ya ce yana daukan darasi daga wasu shahararrun malaman addinin Musulunci kan kowane al'amari na mulki, musamman na Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

"Ni kullum ina daukan darussa daga jawaban wasu shahidai biyu da suka gabatar gabanin mutuwarsu, wato Sheikh Jafar Adam da Sheikh Albani. Sun ce 'yan Najeriya za su fito su yi addu'a, su yi azumi, su yi gwagwarmaya kan Allah ya kawo Muhammadu Buhari kan mulkin Najeriya."

Ya kara da cewa, malaman biyu sun ce, "Shugaba Buhari ba zai san zurfin barnar da aka yi a Najeriya ba sai bayan ya hau karagar mulkin ƙasar. kuma za a sha wahala kafin gyaran da zai yi zai samu, har ya dore yayi wa al'umma amfani."

Sai ku latsa alamar lasifika da ke jikin hoton Gwamna Buni a sama domin jin cikakkiyar hirar da yayi da Ibrahim Isa na BBC Hausa.