Rundunar SWAT da SARS: Masana tsaro sun ce an ƙi cin biri an ci dila

IGP Muhammed Adamu

Asalin hoton, NPF

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya kafa wata sabuwar runduna da za ta maye gurbin rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS.

Sabuwar rundunar ita ce SWAT, wato Special Weapons and Tactics a Turance.

A wata sanarwa wadda mai magana da yawun 'yan sandan Najeriya Frank Mba ya fitar, ya bayyana cewa za a yi wa dakarun da za su yi aiki ƙarƙashin rundunar SWAT gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa da sauran gwaje-gwaje na asibiti domin tabbatar da cewa za su iya gudanar da wannan sabon aikin.

Mece ce rundunar SWAT?

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya bayyana cewa rundunar SWAT za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da SARS take yi.

Amma duk wanda zai kasance ƙarƙashin rundunar, dole ne a yi masa gwajin ƙwaƙwalwa da kuma sauran gwaje-gwaje don sanin ko za su iya gudanar da ayyukan rundunar yadda ya kamata.

Ya ce dakarun rundunar daga rundunonin da ke Kudu Maso Gabashi da Kudu Maso Kudanci za su samu horo a Kwalejin Koyar da Yaƙi da Ta'addanci da ke Nonwa-Tai a jihar Rivers.

Su kuwa dakaru daga rundunonin Arewaci da Kudu Maso Yammaci za su samu nasu horon ne a Kwalejin Horas da 'Yan sanda da ke Ende, jihar Nasarawa da takwararta da ke Ila-Orangun, jihar Osun, in ji sanarwar.

Defunct FSARS

Asalin hoton, OTHER

Akwai bambanci tsakanin SWAT da SARS?

Mutane da dama musamman a shafukan sada zumunta sun fito sun nuna rashin goyon bayansu kan wannan sabuwar runduna ta SWAT da aka kafa da za ta maye gurbin SARS, inda suke cewa hakan tamkar an koma gidan jiya ne.

Wannan dalili ne ya sa BBC ta tuntuɓi Group Captain Saddik Shehu mai ritaya, wani mai sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya, inda ya bayyana cewa bambancin SARS da SWAT suna ne kawai amma ba wani bambanci na a zo a gani.

Ya ce a kowace ƙasa dama ana samun 'yan sanda kashi-kashi, akwai na sasanta jama'a, da na kwance bam da daƙile fashi, wanda hakan ya sa horon da ake bai wa wasu 'yan sanda ya sha bamban da na yau da kullum.

"Amma idan ana maganar SWAT na ƙasashen waje, ba kowane ɗan sanda ba ne zai iya shiga wannan rundunar ba saboda akwai horo na musamman da makamai na musamman da suke amfani da su, da suka haɗa da na huda gini da na bam da na'urori daban-daban.

''Ni a ganina shugaban 'yan sandan Najeriya ya yi azarɓaɓi wajen kafa wannan SWAT ɗin, saboda ina kayan aiki na musamman da ake bai wa SWAT ɗin, ina horon da aka yi musu?'' In ji Group Captain Saddik.

Ya ce ce-ce-ku-ce ne kawai ya yi wa shugaban 'yan sandan yawa da matsin lamba ya sa ya kafa wannan rundunar cikin gaggawa.

"Tun da gwamnati ta rushe SARS, sai a tsaya a yi tunani kafin a san abin da za a fito da shi, amma a ce an rushe SARS jiya, yau da safe a ce an tashi an koma SWAT, kafa SWAT ba ƙaramin aiki ba ne," in ji shi.

A demonstrator holds a banner during a protest against alleged police brutality, in Lagos, Nigeria

Asalin hoton, Reuters

Kan batun gwajin lafiyar ƙwaƙalwa da aka ce za a yi wa 'yan sandan na SWAT, Group Captain Saddik ya ce hakan zai yiwu amma gwajin na buƙatar kuɗaɗe da yawa kuma yin gwajin tamkar "ihu bayan hari ne", in ji shi.

"Ɗan sanda da za ka ba bindiga wanda doka ta ba shi damar raunata ɗan ƙasa ko ma ya kashe shi, ya kamata a ce tun daga farko an yi masa wannan gwajin hankalin kafin a ɗauke shi, ba sai yanzu da aka rushe rundunar ba".

A cewarsa, nan gaba ko soja ko ɗan sanda duk wanda za a ɗauka aiki, ya kamata a duba lafiyar ƙwaƙwalwarsa da kyau.

Wanne hali 'yan sandan rundunar SARS da aka rushe ke ciki?

Kakakin rundunar 'yan sandan ta Najeriya ya ƙara da cewa babban sufeton 'yan sandan ƙasar ya bayar da umarni ga dukkan dakarun SARS da aka rushe su tafi hedikwatar rundunar da ke Abuja inda za a yi musu bayani sannan a gwada lafiyar ƙwaƙwalwarsu da ta lafiyar jikinsu.

"Ana sa ran yin gwajin kan dakarun ne domin kintsa su wajen samun ƙarin horo da wayar da kai kafin a sake tura su don gudanar da aikin ɗan sanda," a cewar sanarwar.

Woman holding a bell

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, The protesters were expressing their frustrations with the police and the state in general

A ƙarshen makon jiya ne Babban Sifeton 'Yan Sandan Najeriya ya soke rundunar SARS bayan jerin zanga-zangar da aka ɗauki kwanaki ana yi a wasu jihohin ƙasar.

'Yan ƙasar suna zargin rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa'ida ba da saɓa dokokin aiki.