Sars: Matasan Najeriyar da suka tilasta wa Shugaba Buhari miƙa wuya

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
Yaɗuwar zanga-zanga kan adawa da sashen da ke kula da fashi da makami na rundunar ƴan sanda wata alama ce da ke nuna cewa matasan ƙasar suna nemar wa kansu muryar da za su buƙaci sauye-sauye a ƙasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Afrika, wacce ake alaƙanta ta da cewa babu shugabanci na gari tun shekara 60 da suka gabata bayan samun ƴancin kai.
Duk da cewa sun tursasa wa shugaban ƙasa ya rusa sashen, ba su gamsu 100 bisa 100 ba, saboda su buƙatarsu ita ce a yi wa rundunar ƴan sanda baki ɗaya garanbawul sannan a gurfanar da jami'an da ke cin zarafin mutane gaban ƙuliya.
Amma abin ya wuce haka saboda yaɗuwar da zanga-zangar ke yi ya bai wa wasu matasan ƙasar damar nemar wa kansu mafita kan lamarin.
Matasa wasu da zane a jikinsu, wasu sun ɓula hanci yaytin da wasu sun rina gashinsu kawai ake gani a kan tituna suna zanga-zangar.

Asalin hoton, Reuters
Akasarinsu shekarunsu na haihuwa daga 18 zuwa 24 ne, wadanda a iya tsawon rayuwarsu ba su taba ganin wadatacciyar wutar lantarki da kuma ilimi kyauta ba. Kana suka shafe shekarun karatun jami'o'insu cikin tsaiko saboda yawan dogon yajin aikin malaman jami'o'i ke yi a kai a kai.
Damuwarsu game da hukumar 'yansanda wata manuniya ce na damuwar da suke da ita gane da ita kan ta gwamnati.
"Abinda na karu da shi a kasar tun lokacin da aka haife ni? daya daga cikin masu zanga-zangar a Abuja babban birnin tarayya Victiroa Pang mai kimanin shekaru 22 wacce ta kammala karatun jami'a ta tambaya, - kana daya daga cikin mata da dama ne da ke kan gaba-gaba a jerin zanga-zangar.
"Iyayenmu sun fada mana cewa akwai lokacin da ya wuce a baya da komai ke tafiya daidai, amma mu ba mu taɓa gani ba,'' ta ce.
Me yasa aka nuna ƙin jinin rundunar Sars?
Galibi jami'an ƴan sanda a Najeriya na da babban tabo wajen karɓar cin hanci da cin zali da rashin mutunta hakkin dan adam, amma kuma mutane sun fi nuna ƙin jinin rundunar ta Sars, wacce ke tafiyar da aikinta musamman wajen cin zarafin matasa.
Wabi rahoto da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar cikin watan Yuni ya nuna a ƙalla mutum 82 da aka azabtar, cin zarafi da kisa ba tare da gurfanarwa ba tsakanin watan Janairu 2017 da Mayun shekara ta 2020.
"Hukumomin Najeriya sun gaza hukunta jami'in ɗan sanda daya duk kuwa da dokar hana azabtarwar da aka gabatar a shekara ta 2017 da kuka shaidun da suka nuna yadda jami'an ƴan sandan ke azabtar tare da cin zarafi wajen tatsar bayanai daga wanda ake zargi da aikata laifi,'' masu zanga-zangar suka ce.

Asalin hoton, Reuters
Wadanda ke yin ''ƙwalisa'' ko ke da farcen susa- kama daga mallakar mota mai tsada da na'urar komfuta ko kuma wadanda ake yi wa zanen jiki ko kuma kitson dada - na jan hankulan jami'an rundunar ta Sars.
Zargin matasa a Najeriya abu ne da ya ta'azzara a cikin al'umma.
Matasan da ke da farcen susa, da kuma yanayin rayuwarsu bai yi daidai da irin yanayin kasa mai ra'ayin mazan jiya irin Najeriya ba a kan yi musu laƙabi da "Yahoo-Boys" - wani salo da ake laƙaba wa masu damfara ta yanar gizo.
Wannan musamman da gaske ne ga wadanda ke aiki da ƙananan komfuta, yayin da akwai maƙwabtansu da ke yi wa matasan da ke aiki daga gida cunen jami'an ƴan sanda.
"Mazauna rukunin gidajen da nake sun taɓa kiran jami'an ƴan sanda su zo su tafi da ni saboda a ko da yaushe ina gida kuma na kan kunna janareta, ina kuma cikin kwanciyar hankali,'' in ji Bright Echefu, mai shekara 22 da ke sarrafa shafukan yanar gizo, da shi ma ya shiga zanga-zangar a Abuja, ya shaida wa BBC.

Asalin hoton, Reuters
An dade wasu iyalai, addinai, al'ummomi har ma da makarantu na danganta rashin mutuntaka ga zanen jiki da huji da kitson dada ko kuma gudanar da wata sana'a da ta sha bamban da wadda aka sani.
"Ta yaya yin zane a kafaɗa za ta saka in zama mai aikata laifi?'' Wata ɗaliba Joy Ulo ta tambaya a yayin zanga-zangar.
Shugaba Muhammadu Buhari, mai shekara 77, wanda a baya ya bayyana wa kafafen yada labaran kasashen waje cewa matasan Najeriya a matsayin ''malalata'', ya sake yin kira ga waɗanda suka shuga matsain tattalin arziki sakamakon dokar kullen cutar korona da su koma gona tun da suna da jini a jika.
Haɗin kai
Duk da cewa akwai alamun hadin kai, mutanen da ta bayyana cewa su suka shirya daukar matakin a kafafen sada zumunta ba sa son a bayyana su a matsayin jagorori.
Sun riga sun shirya komai daga ruwan sha, tutoci, da kuma shirya yadda za a yi belin wadanda aka cafke.
An tara kudin ne ta hanyar gudunmawar jama'a - wata gudumawar an samu daga kasashen waje da akasari daga kamfanonin fasahar sadarwar da galibi da ma'aikatansu ne suka fi samun kansu cikin wannan matsala da jami'an runduna ta Sars.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Masu tsare-tsaren sun ki amincewa su zabi shugabannin kungiyar, sun ce ba sa son kowa ya yi zaman tattaunawa da gwamnati a bayan idonsu, kamar yadda shugabannin ƙwadago wacce ke da tabon kiran janye yajin aiki bayan tattaunawa da jami'an gwamnati ba.
Amma a gaskiya, akasarin nasarorin zanga-zangar sun fi komawa ga taurarin kafafen sada zumunta da taurari, - sabbin taurari wadanda shafukan Instagram da Snapchat da Twitter suka fito da su.

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta

Zanga-zangar wacce aka gudanar akan titina, ta tara jama'a da dama a ranar Larabar da ta gabata kana ta kara kasaita a ranar Alhamis din da ta gabata, bayan da wasu mawaka Runtown da Falz suka shiga ciki.
Amma zanga-zangar ta kara kasaita daga bisani, bayan da wata mata mai suna Rinu ta ja hankulan masu zanga-zangar da su kwana a wajen fadar gwamnatin jihar Lagos.
Bayan da taurari suka yi amfani da muryoyinsu ga maudu'in #EndSARS wato '' kawo karshen rundunar Sars'', ya kara tagomashi a shafin Twitter tare da janyo goyon baya da tallafi daga 'yan kwallo mazauna Burtaniya kamar su Mesut Ozil da Marcus Rashford, da mawaka da taurarin fina-finai.
Shararrun mawakan nan 'yan Najeriya da suka shahara a duniya kamar Wizkid da Davido, da suma suna cikin sa'annin masu zanga-zangar, sun fito a biranen London da Abuja - inda ganinsu ya dakatar da jami'an ƴan sandan daga yin harbi kan masu zanga-zangar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2

Masu zanga-zangar sun kuma fatattaki manema labarai na cikin gida daga dandalin, suna mai zarginsu da yin kwaskwarima game da maudu'in na gangamin a kori rundunar ta Sars, suna bayar da labari na daban ga wadanda ba sa kan yanar gizo.
"Wannan wata fafutuka ce ta ƙin jinin kafa hukuma ne,''Mr Echefu.
"Kana bayanmu ko kuwa akasin haka, babu wani munafurci,'' ya ce.
Masu zangaz-zanga da dama sun ce sun bijirewa gargadin da iyayensu da ma'aikatunsu suka yi musu na kada su shiga zanga-zangar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3

Babu sauran matasan da ba su san ciwon kansu ba
Akwai wadanda da ke jin cewa wannna wata alama ce ta wani abu na musamman a Najeriya a cikin watan da kasar ta yi bikin cika shekaru 60 da samun 'yancin cin gashin kai.
Fiye da kashi 60 bisa dari na matasan Najeriyar 'yan kasa da shekara 24 ne, kamar yadda kiyasin yawan al'umma na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.
Amma an dade ana zargin matasan da ɓata lokaci wajen kallon wasan kwaikwayo na talabijin, kwallon kafa da mu'amala da shafukan sada zumunta- a maimakon mayar da hankali wajen al'amuran da suka shafi mulki.

Asalin hoton, Reuters
Wani ɓangare ne da akasarinsu suka saba ji daga manya, amma kuma bayan da suka tilasta wa shugaban kasa ya soke rundunar Sars da aka sanar kai tsaye a gidan talabijin, matasan za su gane cewa ashe suna da karfin sauya al'amura.
"Jama'ata, ina son wannan sakon ya isa ga dukkanin 'yan Najeriya. An saurari muryoyinku,'' in ji Wizkid a zanga- zangar ranar Lahadi a birnin London.
"Kada ku bari wani ya fada muku cewa ba ku da ikon a ji kokenku. Kuma na muryoyi! Don haka kada ku ji tsoron fitowa ku yi magana''.
"A zabe mai zuwa na shekara ta [2023] za mu nuna karfin fada ajin mu,'' ya ce.











