SARS: Shin da gaske gwamnati take kan batun sauya fasalin ƴan sandan SARS?

Sufeton ƴan sandan Najeriya

Asalin hoton, @PoliceNG

Lokacin karatu: Minti 4

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adam ta Amnesty International ta ce suna da hujjojin da ke nuna cewa gwamnatin Najeriya ba da gaske take ba wurin gyara ayyukan rundunar 'yan sanda ta SARS mai yaƙi da 'yan fashi da manyan laifuka.

Ƙungiyar na mayar da martani ne game da sanarwar da Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya bayar a ranar Lahadi na haramta wa SARS da sauran rundunoni na musamman kafa shingayen bincike a kan titunan ƙasar.

Wannan ya biyo bayan koken da dubban 'yan Najeriya suka yi ne na kiran a rushe SARS saboda zargin da ake yi wa dakarunta na kashe mutane ko kuma azabtar da su da kuma karɓar cin hanci a wurin masu ababen hawa.

Mai magana da yawun Amnesty a Najeriya, Malam Isa Sanusi ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta daɗe tana cewa za ta sauya fasalin rundunar amma ba su ga wani sauyi ba.

"A 2015, sufeton 'yan sanda ya ce za a yi gyara, a 2018 mataimakin shugaban ƙasa ya kafa kwamiti domin sake nata fasali, a 2019 ma Sufeto Janar Mohammed Adamu ya ce za a yi gyara amma abin bai yiwu ba," in ji Isa Sanusi.

Ya ƙara da cewa: "Idan mutum ya ce zai gyara abu sau uku kuma bai gyara ba to kana da hujjar cewa ba da gaske yake ba."

Amnesty ta ce abin da take buƙata shi ne "a kama duk wanda suka aikata laifuka sannan a yi musu shari'a bisa adalci kuma gwamnati ta fayyace wa jami'an tsaro ƙarara cewa ba za ta lamunci take haƙƙin ɗan Adam ba".

Umarnin da aka bai wa SARS

SARS

Cikin sanarwar da shafin Twitter na rundunar ƴan sandan Najeriya ya wallafa a wasu jerin saƙwanni ranar Lahadi, sufeton ƴan sandan ya haramta wa dukkanin rundunoni na musamman da suka haɗa da FSARS da STS da IRT da ke yaƙi da ƙungiyoyin asiri kafa shingayen bincike domin tarewa da binciken ababen hawa.

Sannan an haramta wa duk wani jami'in ƴan sanda fitowa da kayan gida ba tare da kayan ƴan sanda ba. Sanarwar ta ce wasu jami'an na fakewa da wannan suna yin abubuwan da ba su dace ba da suka saɓa doka.

Babban Sufeton ƴan sandan ya kuma yi gargaɗi ga rundunonin game shiga haƙƙin sirrin rayuwar mutane musamman bincike wayoyinsu na salula da kwanfuta da sauran na'urori ba tare da wani samun izini ba.

Sanarwar ta ce an kama wasu daga cikin jami'an SARS da ake zargi da cin zarafin mutane a Legas, sannan za a ci gaba da bincike kan zargin cin zarafi da wasu jami'an rundunar SARS suka aikata.

An buƙaci jami'an su mayar da hankali ga laifukan da suka shafi fashi da makami da satar mutane da sauran muggan laifukan da aka kafa rundunonin domin su, ba su koma cin zarafin al'umma ba.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

'Yan Najeriya sun nuna ɓacin ransu

Dubban 'yan Najeriya ne suka hau shafukan sada zumunta tun daga daren Asabar domin nuna bacin ransu da kuma yin kiran da a kawo ƙarshen ayyukan rundunar, inda suka riƙa amfani da maudu'ai irinsu #EndSARS #EndSarsSNow #EndPoliceBrutality.

Dukkanin maudu'an uku na cikin waɗanda aka fi tattaunawa a kansu a dandalin Twitter.

Wannan matakin da rundunar ƴan sandan Najeriya ta ɗauka ya biyo bayan bidiyo da dama da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda jami'an rundunar ta SARS ke cin zarafin mutane ta hanyar ƙarbar kuɗi har ma da harbin mutane.

Ɗaya daga cikin bidiyon da ke yawo a kafofin sadarwa na intanet ya nuna yadda aka cacumi wani mutum da aka jefa a mota aka tafi da shi.

Tun da farko gwamnatin Jihar Legas ta ce za ta ɗauki mataki kan jami'an rundunar ta musamman mai yaƙi da fashi da makami da ta SARS.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

"Rahotannin yin ƙwace daga mutanen da aka ɗauka domin su kare al'umma abu ne mai tayar da hankali," in ji Gwamna Sanwo-Olu a wani saƙon Twitter.

"Ina tabbatar muku cewa za a ɗauki matakin da ya dace kuma cikin gaggawa."

Tuni da ma ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta yi kiran da a soke ayyukan rundunar sakamakon kisan babu gaira ba dalili da azabtar da waɗanda ake zargi da laifi.

Duk da cewa Gwamna Sanwo-Olu ya yi alƙawarin ɗaukar mataki, sai dai rundunar tana aiki ne a ƙarƙashin Gwamnatin Tarayyar Najeriya, abin da ke nuna cewa babu tabbaci kan irin matakin da gwamnan zai ɗauka.

Babban sufeton ƴan sandan Najeriya ya jaddada ƙudirinsa ga ƴan Najeriya na gyara ayyukan rundunar ƴan sanda wacce za ta kasance mai aiki da kare ƴancin ƴan kasa da kuma kiyaye haƙƙokin da tabbatar da tsaron al'umma.

Ya yi kira ga ƴan Najeriya kada su bari ɗabiun wasu tsirarun jami'an ƴan sandan su tasiri ga imani da amince da suke da shi ga rundunar ƴan sanda.

Labarai masu alaƙa: