Hotunan yadda aka yi ɗaurin auren Aliyu Atiku Abubakar da Fatima Nuhu Ribadu

Asalin hoton, madailygist.ng
An ɗaura auren ɗan tsohon mataimakin shugaban Najeriya Aliyu Atiku Abubakar da amaryarsa Fatima Ribadu, ƴar Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC.
Auren wanda aka ɗaura ranar Asabar, ya samu halartar manyan jiga-jigan ƴan siyasa a Najeriya daga manyan jam'iyyun siyasar ƙasar APC da PDP da suka ƙunshi jagororin jam'iyyun da kuma gwamnoni da minitoci da sauran manyan ƴan siyasa.
Auren ya shafi ɓangarorin jam'iyyun guda biyu inda uban ango Atiku Abubakar ɗan jam'iyyar PDP, yayin da kuma uban amarya Nuhu Ribadu ɗan APC.
Ango Aliyu Atiku Abubakar, shi ne Turakin Adamawa, inda ya gaji babansa Atiku ɗan takarar shugaban ƙasar ƙarƙashin jam'iyyar PDP, bayan da ya zama Wazirin Adamawa a shekarar 2017.
Fatima Ribadu, ɗaya daga cikin ƴaƴan Nuhu Ribadu ce, tsohon shugaban hukumar EFCC.
Bayan ɗaurin auren Atiku Abubakar ya yi godiya a Twitter ga waɗanda suka halarci ɗaurin auren.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Hotunan ɗaurin auren

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, @Atiku

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, @Atiku

Asalin hoton, @Atiku

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai







