Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da makwabtanta.
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba and Awwal Ahmad Janyau
Rufewa
Nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye game da abubuwan da ke faruwa a duniya.
Da fatan za ku kasance da BBC Hausa a gobeAsabar inda za mu ci gaba da kawo abuwawan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ya tsarin karatu zai kasance a Najeriya bayan sanar da ranar buɗe makarantun?
Korona na ƙara kama fitattun mutane da suka ziyarci fadar White House
An samu ƙarin wasu
fitattun mutane da suka kamu da korona a Amurka.
Daga cikinsu akwai
Sanata Mike Lee, wanda ya ce gwaji ya tabbatar da ya kamu da korona bayan ya
ziyarci Fadar White House.
Sanatan na Republican
ya killace kansa na tsawon kwana 10.
Shugaban Jami’ar
Notre Dame John Bennett shi ma ya kamu da korona. Shi ma ya kamu da korona ne
bayan ya ziyarci Fadar White House a ranar Asabar.
Kafofin yada labaran Amurka
sun bayyana damuwa game da ma’aikatan White House, inda yawancinsu ke jiran
sakamakon gwajin korona.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump ya shiga ruɗani
Asalin hoton, Getty Images
Kamuwa da cutar
korona da Trump ya yi ya jefa kwamitin yaƙin neman zaɓensa cikin rudani.
Kwamitin ya sanar
da soke dukkanin tarukan da Trump zai yi ko kuma tunanin sauya su zuwa ta
hanyar intanet.
Fadar White House
ta ce ƙananan alamomin cutar ne kawai Trump ya nuna kuma yana ci gaba da aiki a
killace.
Fadar White House
ta ce shugaban ya ce yana son yi wa Amurkawa jawabi, kuma nan ba da daɗewa ba
za su ji shi.
Trump ya kamu da korona ne tare da uwar gidansa Melania wacce ita ma ta killace kanta.
Jawabin Buhari: Atiku ya mayar da martani
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya mayar wa shugaba Buhari da martani kan jawabinsa na bikin cika shekaru 60 da samun ƴancin kan Najeriya.
A cikin jawabinsa, shugaba Buhari ya zargi shugabannin da ya gada daga 1999 zuwa 2015 da ƙoƙarin durƙusar da Najeriya, inda ya ce ba su da bakin sukar gwamnatinsa.
Amma a martaninsa Atiku babban mai hamayya da Buhari a zaɓen 2019, ya ce "tsakanin 1999 zuwa 2007, ba a bin Najeriya bashi"
Ya kuma ce yana alfari da ayyukan da shi da shugaba Obasanjo suka yi wa kasarsu Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Dakarun Azerbaijan na ci gaba da luguden wuta a yankin Nagorno Karabakh
Asalin hoton, Reuters
Dakarun Azerbaijan na ci gaba da luguden wuta a Ste-pa-nakert babban birnin yankin Nagorno Karabakh da ya ɓalle yayin da aka shiga rana ta shida da farmakin da suka kai wa ƴan Amnenia.
Wakilin BBC da ke garin ya ce mutane na samun mafaka a cikin gidajen kasa.
Babu wata alama da ta nuna cewa ɓangarorin biyu za su kawo ƙarshen yaƙin da suke yi da juna.
Azerbaijan ta ce ba za ta dakatar da buɗe wuta ba idan dakarun Armenia ba su janye daga Nagorno Karabakh ba, a ɗayan bangaren ita ma Armenia ta ce ba za ta zauna akan teburin sulhu ba idan Azerbajan ba ta kawo karshen farmakin da take kaimata ba.
Kakakin rundunar sojin Armeniya ya ce a cikin mitunna da suka wuce an ji karar fashewar wani abu a wani wuri mai nisan kilomita shida daga inda da muke.
Joe Biden bai kamu da cutar korona ba
Asalin hoton, Getty Images
Babban abokin hamayya na Donald Trump na jam'iyyar Democrats a zaɓen shugaban kasa da za a yi a watan gobe, Joe Biden da mai dakinsa ba sa dauke da kwayar da cutar korona.
Mr Biden wanda ya tabbatar da bayanin da likitansa ya yi tun farko, ya ce fatansa shi ne wannan zai tunatar da mutane a kan muhimanci amfani da takunkumin fuska da wanke hannu da sabulu da kuma ba da tazara.
An rika tsamanin rayuwar Mr Biden na cikin hadari saboda sun yi mahawara mai zafi a dandamali daya da Donald Trump a ranar Talatar da ta gabata.
Za a gwada amfani da banɗaki na dala miliyan 23 a tashar sararin samaniya
Asalin hoton, NASA
Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka Nasa za ta ƙaddamar da aikin yin banɗaki a sararin samaniya kafin a iya fara amfani da shi nan gaba a tafiya zuwa duniyar wata.
Banɗakin wanda zai lashe kuɗi dala miliyan 23, wanda ke zuƙo najasa daga jikin mutum, za a aika shi tashar sararin samaniya ta hanyar amfani da jirgin ruwan ɗaukar kaya.
Nasa ta ce famfunan da ke zuƙo abu na banɗakin an tsara shi ne ta yadda mata ƴan sama jannati za su ji daɗin amfani da shi, ba kamar tsohon tsarin ba.
An so a harba rokar da ke ɗauke da jirgin ruwan dakon kayan ne daga Tsibirin Wallops da ke Virginia a ranar Alhamis.
Amma shirin ya gamu da cikas minti uku kafin harbawar saboda matsalolin na'ura da aka samu.
Za a sake gwada harbawar a yau Juma'a da yamma idan har injiniyoyi suka gyara matsalolin da suka jawo tsaikon na ranar Alhamis.
Asalin hoton, NASA
Asalin hoton, NASA
Shugaban Faransa ya yi alƙawarin karya lagon 'matsalar yaɗa akidar amfani da Musulunci' wajen raba kan al'umma
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba
Macron ya yi alƙawarin karya lagon, a kan abin da ya kira matsalar yaɗa akidar
amfani da Musulunci wajen raba kan al'umma a Faransa.
A wani jawabi a
wajen birnin Paris, ya ce wasu 'yan kalilan daga cikin Musulmin Faransa
kimanin miliyan shida na da alamun gina wata al'umma kishiyar jamhuriyya
ta Faransa, wadda ba a haDa ta da addini, don haka ya ce akwai buƙatar kafa
tsauraran dokoki domin daƙile aikace-aikacensu.
A Matakan da shugaban ya bayyana za a
samar da doka da za a miƙa wa majalisar dokokin kasar, kafin ƙarshen
wannan shekarar.
Daga cikin tanade-tanaden dokar, akwai tsattsauran sa ido da lura kan harkokin wasanni da sauran
kungiyoyi, ta yadda ba za su zama wasu wurare ko dandali da masu tsattsaurar
akida za su rika koyar da manufofinsu ba.
Sannan akwai kawo karshen tsarin aikawa da Limaman
Musulunci zuwa Faransar daga wasu kasashe na waje, da sanya ido sosai a kan masallatai, ta
yadda ba za su faɗa hannun masu tsattauran ra’ayi ba, da kuma kawo ƙarshen tsarin koyar da yara a gida.
Sai dai kuma ana ganin batun hana karantar da yara a gidan zai zama wani abu da zai jawo taƙaddama saboda yara wajen dubu hamsin da
aka yi ƙiyasi ana koyar da su ba a makaranta ba a kasar ta Faransa, wato a gida a yau, yawancinsu ba su da wata alaƙa sam-sam da
addinin Musulunci.
Jawabin na Shugaba Macron ya biyo bayan tattaunawa ce ta tsawon watanni
da suka yi da shugabannin addinai da masana, kuma fadar gwamnatin ƙasar na nuna hakan a matsayin wata alama ta cewa shugaban na son yin magana a bayyane ba tare da wani shakku a kan hadarin
tsattsaurar akidar Musulunci ba.
Sai dai ‘yan kasar da dama na kallon jawabin a matsayin wata siyasa
kawai, da shugaban ke gabatar da kansa a matsayin mai kishi ko kare kasar ta
Faransa, ta wata hanya da zai kara kwantawa a ran masu zabe ‘yan ra’ayin
riƙau, sannan kuma ya kara farin jininsa domin zaben da ke tafe na shugaban
kasa a shekara ta 2022
An haramta wa mataimakin shugaban Kenya shiga ofishin jam'iyya mai mulki, Daga Emmanuel Igunza BBC News, Nairobi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaba Uhuru Kenyatta (hagu) da mataimakinsa William Ruto sun kafa gamayya a 2012
Jam'iyya mai mulki a Kenya - Jubilee - ta haramta wa mataimakin shugaban ƙasar William Ruto shiga hedikwatar jam'iyyar yayin da dangantaka tsakanin shugaban da mataimakinsa ke ci gaba da yi tsami.
Sakatare Janar na jam'iyyar Raphael Tuju ya yi iƙirarin cewa mataimakin shugaban kasar ya fice daga jam'iyyar bayan ƙaddamar da hedikwatarsa ta ƙashin kai domin bunƙasa ƙudirinsa na zama shugaba a 2022.
Cikin bainar jama'a, shugaban da mataimakinsa sun yi watsi da rahotanni kan tsamin dangantakar da ke tsakaninsu amma mataimakansu sun fitar da sanarwa da ta tabbatar da banbancin da ke tsakaninsu.
A wannan makon, mataimakin shugaban bai halarci taron ƙasar da shugaban ya halarta ba - inda kujerarsa ta zama ba kowa a kai har ƙarshen taron.
Lamarin ya sa fargaba kan afkuwar irin rikicin da ya faru a 2007 - rikicin da ya halaka mutum 1,000.
Joe Biden ya mika saƙon jaje ga Trump
Babban abokin hamayyar shugaban Amurka a zaɓen watan Nuwamba Joe Biden ya wallafa wani saƙon Tuwita game da Donald Trump.
Cikin saƙon, Biden ya ce "Ni da Jill na miƙa saƙon samun sauƙi ga shugaba Trump da Melania. Za mu ci gaba da yi musu addu'a".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Buhari ya yi wa Trump addu’a
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bi sahun al'umar Amurka wajen yi wa Donald Trump da mai dakinsa addu'ar samun sauki bayan sun kamu da cutar korona.
Shugaban ya ce kamuwa da cutar da Trump ya yi ya nuna irin ƙalubalen cutar a duniya da kuma matsalar kawar da ita.
Cikin sanarwar da mai taimaka wa shugaban Najeriya Garba Shehu ya fitar, Buhari ya sake nanata buƙatar bin shawarwarin likitoci game da cutar ta korona.
Shugaban WHO ya aike sakon fatan alheri ga Trump
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya aike da saƙon fatan alheri tare da addu'ar samun sauƙi ga Shugaban Amurka Donald Trump da mai ɗakinsa a shafinsa Tuwita.
Tun farko Trump ya sha caccakar WHO kan yadda take tafiyar da annobar. A farkon wannan shekarar, Trump ya sanar cewa zai kawo ƙarshen alaƙar ƙasarsa da WHO inda ya yi iƙirarin cewa hukumar tana ƙarƙashin ikon China inda cutar ta samo asali.
Amurka ce ƙasar da ta fi bai wa hukumar lafiyar ta duniya wadda take taimaka wa ƙasashe inganta harkokin lafiya da magance barkewar cututtuka.
Masar ta yi amfani da ƙarfin soja kan masu zanga-zanga – Amnesty
Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty International ta ce dakarun Masar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harbi a lokuta daban-daban domin tarwatsa masu zanga-zangar nuna ƙin jinin gwamnati a watan da ya gabata.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ya ce majiyoyinta sun faɗa mata cewa sojojin sun kashe mutum biyu tare da kame ɗaruruwan mutane tare da tilasta wa wasu da dama tserewa gidajensu.
Amnesty ta ce rahotonta ya dogara ne kan tattaunawar da ta yi da waɗanda lamarin ya faru kan idanunsu da lauyoyi da duba wasu hoton bidiyon zanga-zangar da ta faru a wurare da dama a tsakiyar watan da ya gabata.
'Trump ya fara nuna alamomin cutar korona'
Shugaban Amurka Donald Trump yana nuna alamomin cutar korona amma ba masu tsanani ba, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP da rahoton jaridar New York Times.
Tun farko, likitan shugaban ya ce Trump da mai ɗakinsa Melania wadda ita ma ta kamu da korona na cikin ƙoshin lafiya kuma an tsara za su ci gaba da zama a gida cikin harabar White House".
Uganda za ta sallami masu korona ba tare da gwaji ba
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiya ta Uganda ta sake bibiyar ƙa'idojin sallamar masu cutar korona lamarin da zai bai wa mutanen da ba sa nuna alamomin cutar damar barin asibiti ba tare da yi musu gwaji ba.
Ministan lafiya ta ƙasar Jane Ruth Aceng ta ce za a sallami marasa lafiyar da ke killace na tsawon kwana 10 ba tare da wani gwaji idan basu nuna alamomin cutar ba.
Hakan zai rage yawan kwanakin da mara lafiya zai yi kafin a sallame shi bayan gwajin farko.
A baya ana sallamar mara lafiya ne bayan an yi masa gwajin da ya nuna ba ya ɗauke da cutar sau biyu. Amma wasu marasa lafiya sun koka kan lokacin da suka shafe suna jiran sakamakon gwaji duk da cewa basu nuna alamomin cutar ba.
Uganda ya zuwa yanzu ta tabbatar da mutum 8,287 suna ɗauke da cutar har da 4,430 da suka warke sai wasu 75 da suka mutu.
Shugaban Zimbabwe ya yi wa Trump addu'ar samun sauƙi
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya aike sakonsa na fatan alheri ga Shugaban Amurka Donald Trump da matarsa bayan da suka kamu da cutar korona.
Mr Trump da matarsa Melania Trump ya sanar yau Juma'a cewa suna killace kansu kuma likitansu ya ce za su ci gaba da zama a fadar White House lokacin da suke farfaɗowa."
Shugaba Mnangagwa ya aike sako ta shafinsa na Tuwita:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Alaƙa tsakanin ƙasashen biyu ta yi tsami tun bayan da Amurka ta ƙaƙaba takunkumi kan mutane da kamfanonin da ta zarga da take haƙƙoƙin bil adama. Wasu daga cikin takunkuman sun fara ne shekaru 20 da suka gabata.
Shugaba Mnangagwa na daga cikin waɗanda aka ƙaƙabawa takunkumin.
Saurari Labaran Rana cikin Minti Ɗaya
Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar domin sauraron Minti Ɗaya Da BBC Na Rana tare da Buhari Fagge da Nabeela Mukhtar Uba
Malaman Tsangaya sun nuna ɓacin rai a kan matakin gwamnatin Kano game da tsarin ilimin bai ɗaya
Kungiyar malaman Tsangaya a jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan matakin gwamnati na kin saka su a kwamitin da ta kafa, da zai duba yiwuwar shigar da makarantun tsangaya da Islamiyya cikin tsarin ilimin bai daya a jihar.
Gwani Sunusi Abubakar Sakataren Kungiyar makarantun Al-Qur'ani da makarantun tsangayu na ƙasar a jihar Kano ya ce ya kamata gwamnati ta tuntuɓe su sannan ta sanar da su tsarin da take son kawowa, "mu da muke harka ta almajirai bamu san komai ba."
Latsa alamar lasifikar da ke ƙasa domin sauraron rahoton Khalifa Shehu Dokaji.
Bayanan sautiRahoton Khalifa Shehu Dokaji
Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Alli da Aouar da Rudiger da Torreira da Gray
Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta ki amincewa da tayin £1.5m daga wurin Paris St-Germain domin karbar aron dan wasan Ingila Dele Alli saboda haka dan wasan mai shekara 24 zai ci gaba da zama a Ingila.(Guardian)
Amma PSG tana sake shiri domin karbo aron Alli.(Telegraph)
A gefe guda,Tottenham ta nemi karbo aron dan wasan Chelsea da Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 27, kuma an ce kungiyoyin biyu da ke hamayya sun soma tattaunawa kan hakan.(Nicolo Schira, via Express)
Arsenal ta amince ta bai wa Atletico Madrid aron dan wasan Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 24, kuma hakan zai ba ta damar dauko dan wasan Faransa mai shekara 22 Houssem Aouar daga Lyon.(AS, via Mirror)
Paris Saint-Germain za ta iya yin kafar-ungulu ga yunkurin Arsenal na dauko Aouar bayan da ita ma ta bi sahun tattaunawar dauko dan wasan na Faransa.(L'Equipe, via Metro)
Su wa ne suka kasance tare da Trump a wannan makon?
Asalin hoton, Getty Images
Sanarwar Trump ya kamu da cutar korona ta
zo bayan ya shagaltu da gudanar da harkokin mulki da yaƙin zaɓe gabanin zaɓen 3
ga watan Nuwamba wanda a lokacin ya tattauan da manyan jami'ai da dama.
A ranar Litinin, ya yi wani taron ƴan
jarida - inda ya ba da bayanai kan dabarun gwamnatinsa na gwajin cutar korona -
a fadar White House wanda ya samu halartar Mataimakinsa Mike Pence da Sakataren
lafiya Alex Azar da Sakataren ilimi Betsy DeVos da kuma wasu.
A muwaharar da aka yi ranar Talata, Shugaba
Trump ya tsaya a mumbari tare da abokin hamayyarsa Joe Biden amma yana tare da
manyan mataimakansa ciki har da shugaban ma'aikata a fadar White House Mark
Meadows da mai tsara yaƙin zaɓensa Jason Miller da kuma mai ba shi shawara
Stephen Miller.
Duk ƴaƴansa - da abokan zamansu - sun
kasance tare da shi. Kuma bayanai na cewa babu wani a cikinsu da ya sa
takunkumi yayin tafka mahawarar.
A dai makon, matar da ya zaɓa a matsayin
alƙaliyar Kotun Koli - mai shari'a Amy Coney Barrett - ita ma ta ziyarci Fadar
White House.
Yana daukar kwanaki biyar daga lokacin
da mutum ya kamu da cutar ya fara nuna alamunta, amma Hukumar Lafiya ta Duniya
WHO ta ce ana iya daukar kwanaki 14.