Hotunan yadda ƴan Shi'a suka yi bikin ranar Ashura a duniya

Asalin hoton, @ihrc
Gargaɗi: Akwai hotunan da za su ɗaga hankali
Mabiya Shi'a sun yi jimamin ranar Ashura a sassan duniya daban-daban, inda suka fito kan tituna don nuna alhini kamar yadda suka saba a zagayowar ranar da Imam Hussein jikan Annabi Muhammad (SAW) ya yi shahada a Karbala da ke kasar Iraƙi.
Duk 10 ga watan Muharram ne na kalandar musulunci ƴan Shi'a a sassan duniya ke jimamin shahadar jikan manzon Allah Imam Hussian a yaƙin Karbala kuma duk da annobar Covid 19 amma daruruwan mabiya Shi'a ne suka ziyarci Hubbarensa sanye da baƙaƙen kaya, wasu kuma da takunkumi ba tare da bayar da tazara ba tsakaninsu.
Akwai saɓani tsakanin mabiya Sunna da ƴan Shi'a game da ranar Ashura inda ɓangaren Sunni ke azumi a yinin ranar Ashura yayin da kuma ƴan Shi'a ke jimami.
Cikin kasashen da ƴan Shi'a suka yi bikin Ashura akwai Iran da Iraƙi da Syria da Turkiyya da Lebanon da Najeriya da sauran ƙasashen da ke da mabiya mazhabar Shi'a.
Ga yadda ƴan Shi'a suka yi bikin ranar Ashura

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, IMN

Asalin hoton, IMN

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images







