Marie Bonaparte, matar da ta soma koya wa mata ilimin jima'i

    • Marubuci, Analía Llorente
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo

Ga wasu mutanen, matar ta kasance wadda ta ƙiƙiri ilimin jima'i, ga wasu kuma, suna ɗaukarta kuma a matsayin mace mai kuɗi da ke da hanyoyi daban0-daban.

Maganar gaskiya ita ce Marie Bonaparte wadda aka haifa 1882 ta mutu 1962 tamkar 'ya ta ke ga sarkin Faransa na wancan lokaci wato Napoleon, haka zalika, gwaggon Yarima Philip ce wanda shi ne Duke na Edinburgh.

Wadda itama 'yar sarki ce, babban abin da ta fi mayar da hankali a duniya shi ne gamsuwar mata yayin da suke saduwa.

Wannan ne ya ja ta zama ɗaliba, kuma har a wani lokaci ma ta taɓa ceto Sigmund Freud.

Amma kan a kan komai, Bonaparte mace ce mai 'yanci.

'Yar sarki

An haifi Marie Bonaparte a Paris, kuma ta fito daga babban gida, masu hali.

Ta kasance 'ya ga Marie-Felix(nee Blanc) wanda shi ne yarima Roland Napoleon Bonaparte na Faransa.

Kakanta Francois Blanc, ya kasance ɗan kasuwa kuma wanda ya ƙirƙiro Casino Monte Carlo.

Sai dai ta sha faɗawa cikin bala'i daban-daban tun daga haihuwarta inda ta kusan mutuwa da aka haife ta.

Mahaifiyarta ta mutu wata ɗaya bayan haihuwarta.

Ganin cewa babu wasu yara akusa da ita, ta makale wa mahaifinta - wanda masanin halayyar ɗan adam ne da kuma ilim bayanin ƙasa.

Ta kasance neman ili kan kimiyya da rubutun zube, da jikinta ita kanta.

Wata rana, "Miamau", ɗaya daga cikin matan da ke kula da ita, ta zo ta tarar da Marie trana wasa da al'aurar ta.

"Zunubi me! Idan kina haka, za ki mutu!" ta gaya mata, kamar yadda Marie ta rubuta a cikin littafin sirrinta a 1952.

"Bonaparte ta bayyana cewa ta daina wasa wasa da al'aurar ta lokacin tana da shekaru takwas zuwa tara sakamakon gargadin da Mimau ta yi mata na cewa duk mai wasa da al'aurarsa mutuwa zai yi," kamar yadda Nellue Thompson ta rubuta.

Tun tana ƙarama, ta kasance 'yar tawaye wadda ba ta yarda cewa mata su yi wa maza biyayya ba.

Lokacin tana matashiya, ta fara koyon yare daban-daban - akasari Turanci da Jamusanci - amma kakarta da mahaifinta sun hanata kan cewa kada ta sake yin wata jarabawa.

"Ita da Roland sun dage kan cewa maƙiyan su za su iya yin ƙafar ungulu ga jarabawarta domin su jawo wa iyalan Bonaparte abin kunya," in ji Thompson.

Wannan ne ya jawo Marie ta fusata, "Tir da sunana, da muƙami na da ƙaddarata! musamman don ni mace ce! da ni namiji ce da ba za su hana ni yin jarabawa ba!" in ji Thompson kamar yadda Marie ta rubuta a litaffin sirrinta.

Kafin ta kai shekaru 20, a lokacin da take tashen balagarta, Marie Bonaparte ta taɓa soyayya da wani mutum mai aure, ɗaya daga cikin mataimakan mahaifinta.

Sai dai a ƙarshe ba su kwashe ta daɗi ba, sai aka kwashe da cin mutuncin juna.

Daga baya mahaifinta ya yanke shawarar kawo wa Marie mijin da yake so ta aura, wato Yarima George na Girka da Denmark, wanda ya girme ta da shekaru 13.

Marie ta amince, inda suka yi aure a ranar 12 ga watan Disambar 1907 a birnin Athens.

Sun samu yara uku, Eugenie da Peter, sai dai ba su ji daɗin auren.

Duk da cewa Marie da mijinta sun shafe shekaru 50 a tare, Marie ta gano cewa mijinta ya fi son kawuna Yarima Valdemar na Denmark a kan ta.

Neman ilimi kan sha'awar mata

Buƙatar da Marie ke yi na namiji da kuma neman ilimi kan yanayin sha'awar mata yayin jima'i ya ja ta fantsama neman ilimi.

A 1924, ta wallafa wata maƙala kan rashin gamsuwar mata yayin jima'i.

"Ta damu kan cewa bata taɓa gamsuwa yayin jima'i ba," in ji Kim Wallen, wanda wani farfesa ne a jami'ar Emory da ke Georgia Amurka.

Marie ta yi zaton cewa a duk lokacin da mace ta kasa gamsuwa lokacin jima'i, wata matsala ce daga jikinta.

Sai ta yi wani rubutu wanda ke cewa: rashin nisa tsakanin ɗan tsakar mace da farjin ta, shi ke sa yiwuwar ta samu gamsuwa cikin sauri yayi jima'i.

Domin ta ƙara tabbatar da wannan rubutun da ta yi ko kuma hasashe, sai ta yi bincike kan wasu mata 240 a shekarun 1920 a Paris.

Kamar yadda ta wallafa, " ba a tattaro alƙaluman ba hakanan kawai, an tattaro su ne bisa hujjoji, a duk lokacin da mace ta je ganin likita", in ji Farfesa Wallen, wanda ya yi nazari kan ayyukan da Bonaparte ta yi tare da Dakta Elisabeth Lloyd.

Kamar yadda waɗannan masanan suka bayyana, ta rarraba rukunin mutanen zuwa kashi uku.

"Bonaparte ta yi hasashe mai kyau. Ita ta ƙirƙiro wannan hasashen kan cewa ko wace mace daban take, wanda hakan ya sa kowace da yanayin yadda take gamsuwa yayin jima'i," In ji Dakta Lloyd.

Wannan ne ya sa Bonaparte take ganin cewa idan aka yi wa mace tiyata aka matso mata da ɗan tsakarta kusa da farjinta, hakan zai sa ta rinƙa gamsuwa cikin sauri.

Sai dai wannan hasashen nata bai tafi a banza ba.

"Wannan tiyata bala'i ce. Wasu matan su rasa duka sha'awarsu. Sai dai Marie Bonarte ta kafe kan cewa ta yarda da abin da ta gano, ta amince itama aka yi mata irin wannan tiyatar," in ji Farfesa Wallen.

An yi mata wannan tiyatar kusan sau uku.

"Idan aka yanke jijiyoyi da dama kusa da ɗan tsakar mace, ba za ta rinƙa sha'awa ba yadda ya kamata, sai dai rashin sha'awar ma, sakamakon ana yanke jijiyoyi masu amfani," in ji Dakta Lloyd, wanda ƙwararre ne a ɓangaren tarihi da falsafar kimiyya a tsangayar ilimin hallitu a jami'ar Indiana.

"Ta amince kan cewa tiyata ita kaɗai ce hanyar da za a bi wurin mace ta samu gamsuwa lokacin jima'i," in ji ta.