Gwaggon biri: Biranya na murnar sake haihuwa bayan mutuwar ɗanta

Asalin hoton, PA Media
An haifi wani gwaggon biri a wani gidan zoo na birnin Bristol da ke Ingila.
Masu kula da gidan zoo ɗin dai sun isa gidan ranar Laraba inda suka tarar da jinjirin gwaggon birin mahaifiyarsa ta rungume shi.
Hotunan da aka ɗauka sa'o'i kaɗan bayan haihuwar jinjirin a ranar Laraba sun nuna Kala - wata biranya mai shekaru tara ta rungume sabon jinjirin da ta haifa.
Ma'aikatan gidan zoo ɗin sun bayyana cewa mahaifiyar da abin da ta haifa na cikin ƙoshin lafiya.
Gidan zoo ɗin ya bayyana cewa Kala ta haifi sabon jinjirin nata ne da kan ta ba tare da yi mata tiyata ba.
Kuma ta haihu mijinta na kusa da ita wanda ake kira Jock. A shekarar bara Kala ta haifi gwaggon birinta na farko, sai dai makon sa guda da haihuwa ya mutu.

Asalin hoton, PA Media
Lynsey Bugg, wadda ita ce babbar mai kula da dabbobi a gidan zoo ɗin ta shaida cewa: "Mun san za a haifi jinjirin gwaggwon biri, kuma mun ɗan jima muna sa ido.
"A ranar Talata, Kala ta murmure ta yi kyau kuma da alamu ta kasance cikin natsuwa, haka kuma ba ta yi wani rashin jin magana ba.
"Na zo a safiyar Laraba kawai sai na ga sabon jinjiri a gidan zoo ɗin."

Asalin hoton, PA Media
Ta bayyana cewa ma'aikatan gidan zoo ɗin na cikin fargaba a kullum idan suka tuna da mutuwar jinjirin Kala a Satumbar bara, mako guda bayan an yi wa Kala tiyata an ciro gwaggon birin.
"Wannan wani abu mai kyau ne ganin cewa ta haihu da kanta ba tare da an yi mata tiyata ba kuma uwar da abin da ta haifa na cikin ƙoshin lafiya.
"Uwa ce mai jin magana kuma mai kula da jinjirinta, kuma jinjirin na tsotson mama yadda ya kamata, kuma jinjirin na cike da ƙarfi kuma girmansa ya kai."
Zai ɗauki lokaci kafin gidan zoo ɗin su san ko jinjirin mace ce ko namiji, in ji Ms Bugg.
Wannan sabon jinjirin da aka haifa zai shiga jerin gwaggwon birai shida da ke a gidan Zoo ɗin.
Irin wannan nau'in na gwaggon birin da ke a zoo ɗin na fuskantar barazanar ƙarewa a dazuka, inda wasu ke ƙiyasin cewa adadin waɗanda suka rage a dazukan duniya ba su wuce dubu 100 ba.

Asalin hoton, PA Media











