Gwaggwon birrai a Najeriya: Hotunansu da ba kasafai ake gani ba

Cross River gorillas

Asalin hoton, WCS

Bayanan hoto, An kiyasta gwaggon birrai 300 ne kawai suka rage a dazukan jihar Cross River

Masu fafutukar kare muhalli sun ce a karon farko cikin shekaru an dauki hotunan wasu gwaggon birrai da ke rayuwa a wasu tsaunukan kudancin Najeriya.

Gwaggon birrai 300 ne kawai suka rage a dazukan jihar Cross River wanda ya sa suka zama cikin birrai irinsu na dawa da suka kusa karewa.

Amma kungiyar Wildlife Conservation Society mai rajin kare dabbobin dawa ta ce wannan labarin ya tabbatar da cewa dabbobin na hayayyafa sosai.

An kuma ga wasu kananan gwaggon birrai goye a bayan iyayensu cikin hotunan da aka dauka a farko wannan shekarar.

Cross River gorillas

Asalin hoton, WCS Nigeria

Bayanan hoto, Gwaggon birran - masu son kiriniya sosai - an gan su cikin hotunan da aka dauka a farko wannan shekarar
Cross River gorillas

Asalin hoton, WCS Nigeria

Bayanan hoto, Masu rajin kare muhalli na cewa hotunan sun karfafa mu su gwuiwa ganin yadda suke hayayyafa sosai

Kungiyar WCS in Nigeria - kungiyar kasa-da-kasa ce wadda kuma ba ta gwamnati ce ba - ta ce an dauki hotunan ne bayan da aka dasa wasu na'urorin daukan hoto a kan tsaunukan Mbe.

'Masu gujewa dan Adam'

Birran Cross River na cikin manyan gwaggon birran da ke da wuyar samu a duniya, kamar yadda hukumar World Wide Fund for Nature (WWF) ta ce.

Bincike kuma ya nuna birran na gujewa bil Adama bayan wasu bambance-bambance da suke da su tsakaninsu da sauran gwaggon biri - kananan kawuna da dogayen hannuwa da kuma gashin jikinsu mai hasken launi.

Wadannan birran na rayuwa ne a bisa wasu tsaunuka da ke Najeriya da Kamaru amma ba kasafai a kan gan su ba sai an wahala.

Kungiyar WCS ta ce tana aiki tare da wata kungiya mai suna 'Conservation Association of the Mbe Mountains' da ke fafutukar kare muhalli a tsaunukan Mbe da kuma hukumomin jihar Cross River domin kare gwaggon birran.

A silverback Cross River gorilla

Asalin hoton, WCS Nigeria

Bayanan hoto, Wannan gwaggon birin na cikin wadanda aka yi sa'ar daukar hotonsa a saman tsaunukan Mbe