Akinwumi Adesina: Dalilin da ya sa aka wanke shi daga zargin cin hanci da fifita 'yan Nigeria

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin ne wani kwamiti mai zaman kansa da aka kafa don bincike kan shugaban Bankin Ci gaban Afirka, Africa Development Bank (AfDB), Akinwumi Adesina, ya wanke shi daga zarge-zargen cin hanci da nuna ɓangaranci.
Majalisar gudanawar bankin ce ta kafa kwamitin bayan ƙasar Amurka ta yi ƙorafi game da yadda wasu kwamitoci na manyan mahukuntan bankin suka wanke shi tun farko game da zarge-zargen.
Akinwumi Adesina, ya zama shugaban bankin ne a shekarar 2015 bayan ya ajiye muƙamin ministan aikin gona a Najeriya ƙarƙashin gwamnatin Muhammadu Buhari - daga 2011 zuwa 2015.
Me ya sa aka wanke shi
Kwamitin da ya wanke Mista Adesina yana da mambobi uku da suka haɗa da Mary Robinson, tsohuwar shugabar Ƙasar Ireland a matsayin shugaba, da tsohon shugaban hukumar kare haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya kuma Alƙalin Alƙalai na Gambia, Hassan B. Jallow.
Cikon na ukun shi ne Leonard McCarthy, tsohon mai bincike kuma mai gabatar da ƙara kan laifukan tattalin arziki a Afirka ta Kudu.
"Mun duba amsoshin da shugaban (bankin) ya bayar kuma mun same su ababen amincewa da suke nuna ba shi da wani laifi," a cewar rahoton kwamitin, wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.
Baya ga duba rahoton kwamitin ladaftarwa da suka yi - wanda ya wanke Adesina tun farko - kwamitin mai zaman kansa ya kuma duba dukkanin zarge-zarge 16 da aka yi masa sannan ya duba dukkanin amsoshin da ya bayar game da su.
Ƙasashen da suka fi hannun jari a bankin AfDB
- Najeriya: kashi 9.1 cikin 100
- Amurika: kashi 6.5 cikin 100
- Masar: kashi 5.5 cikin 100
- Japan: kashi 5.4 cikin 100
- Afirka ta Kudu: kashi 4.9 cikin 100
- Aljeriya: kashi 4.1 cikin 100
- Jamus: kashi 4 cikin 100
- Canada: kashi 3.8 cikin 100
- Ivory Coast: kashi 3.7 cikin 100
- Faransa: kashi 3.6 cikin 100
Daga zarge-zargen akwai naɗa 'yan uwansa a kan wasu manyan muƙamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa.
Kazalika an zarge shi da fifita 'yan Najeriya wurin bayar da kwangiloli da kuma sauran ayuukan bankin, Sai dai Adesina ya sha musanta zarge-zargen.
Kwamitin ladaftarwa na bankin ya ce "zarge-zargen ba su da tushe", sannan ita ma majalisar gudanarwar bankin ta amince da rahoton kwamitin farko, inda suka wanke shi daga zargin baki ɗaya.
Amurka ta ce ta damu da harkokin bankin ne saboda ita ce ƙasa ta biyu mafi girman hannun jari a cikinsa bayan Najeriya.
Denmark, Norway, Sweden da kuma Finland - wadanda su ma suna da hannun jari a bankin - sun aike da sakon da ke goyon bayan gudanar da bincike mai zaman kansa a kan Mista Adesina.
Tarihin Akinwumi Adesina a taƙaice
- Shi ne ɗan Najeriya na farko da ya zama shugaban bankin AfDB
- An zaɓe shi a wa'adin farko na tsawon shekara biyar a 2015
- Ministan aikin gona na Najeriya daga 2011 zuwa 2015
- Mujallar Forbes ta zaɓe shi Gwarzon Ɗan Afirka na shekarar 2013 saboda sauyin da ya kawo a bangaren noma
- Wani malamin jami'a a Najeriya ya taɓa ce masa ba zai taɓa shiga Jami'ar Purdue ba saboda bai iya lissafi ba
- Bai bari malamin ya sare masa gwiwa ba, inda ya shiga jami'ar mai daraja da ke Amurka
- Ya ƙi zuwa Jami'ar Cambridge da ake girmamawa bayan ta yarda ta karɓe shi
- Ya yi digirinsa na uku a ɓangaren tattalin arzikin noma a shekarar 1988











