Rikicin ƙabilanci: Me ke faruwa a Kudancin Kaduna?

Nasir El-Rufai

Asalin hoton, Facebook/El-Rufai

Bayanan hoto, Gwamna Nasir El-Rufai ya kafa kwamiti doimin duba wani rahoto na shekarar 1992 kan rikicin Kudancin Kaduna
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau

Yankin Kudancin Kaduna ya yi ƙaurin suna a 'yan kwanakin nan ba don komai ba sai kashe-kashen da ke da nasaba da ƙabilanci da addini da ake yi lokaci zuwa lokaci.

Hakan ya jawo nuna wa juna yatsa tsakanin al'umma biyu mafi girma da ke zaune a yankin; Musulmi da Kirista, inda kowaɗanne ke cewa ana kashe musu 'yan uwa.

Rahotanni na baya-bayan nan na nuna cewa an kashe mutane da dama a yankin, wanda da wuya a iya sanin haƙiƙanin adadin waɗanda suka mutu.

Ko a ranar Asabar rahotannin sun ce an kai hari a ƙananan hukumomin Jema'a da Ƙaura tare da kashe kusan mutum tara.

Gwamna Nasir El-Rufai ya kafa wani kwamiti da zai duba rahoton wani kwamitin da ya yi bincike game da rikice-rikice makamantan waɗannan da aka yi a shekarar 1992 domin yin amfani da shi wurin samar da zaman lafiya.

Gwamnan yana cewa ne rashin magance matsalolin tun daga tushe shi ne abin da ya hana samun tabbataccen zaman lafiya tsakanin ƙabilun yankin.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yayin wani taro da shugabannin ƙungiyoyin Fulani suka yi a Kaduna ranar 3 ga watan Yuni, sun ce Fulani 3,099 ne rikicin ya raba da muhallansu a Kudancin Kaduna.

Ita ma jaridar Punch ta ce wani babban jami'in ƙungiyar CAN - ta Kiristocin Najeriya - a Kudancin Kaduna, Rev. John Cheitnum ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da yin wasarere da rayuwar Kiristoci.

Wannan layi ne

Rikin Kudancin Kaduna ya wuce yadda mutane ke tunaninsa - Fadar Shugaban ƙasa

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Fadar Shugaba Buhari ta ce an tura jami'an tsaro masu yawa zuwa yankin

Fadar Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ta bayyana "cakuɗuwar fashi da ke da alaƙa siyasa da hare-haren ramuwar gayya daga ƙungiyoyin miyagu da ke fakewa da ƙabilanci da addini" a matsayin abin da ke rura wutar rikicin.

Cikin sanarwar da fadar ta fitar ranar 21 ga Yuli, Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Buhari, ya ce "rikita-rikitar da ke Kudancin Kaduna ta fi ƙarfin duk yadda masu sukar gwamnati ke tunani".

"Daga alƙaluman da muka tattara, an tura jami'an tsaro masu yawa Kudancin Kaduna, ciki har da sojoji da dakaru na musamman, na ƙasa da na ruwa, da jiragen tattara bayanai da ke aiki ba dare ba rana domin samar da zaman lafiya," in ji Garba Shehu.

"Abin da ake buƙata daga shugabannin al'ummar yankin shi ne su mayar da hankali wurin tattara bayanan sirri domin bai wa jami'an tsaro ta yadda za su samu damar daƙile duk wani hari da aka shirya kaiwa."

Wannan layi ne

'Rashin adalci ne babbar matsalar'

Shugaban ƙungiyar matasan Fulani ta Bandirako Youth Association of Nigeria, Murtala Ja'afar Jirge ya shaida wa BBC cewa rashin adalci daga sauran ƙabilu ne ke kawo tashe-tashen hankali a yankin.

"Ƙabilun da ke Kudancin Kaduna ba sa yi mana adalci daga kalaman da suke yi," in ji shi. "Idan ma ana kashe musu mutane to ba mu ba ne, don su ma suna rikici tsakanin ƙabilunsu."

Game da shirin da ƙungiyarsu take yi na zaman lafiya kuwa, Murtala Jirge ya ce ya zuwa yanzu mutanensu Fulani kawai suke bi suna bai wa haƙurin abubuwan da aka yi musu.

Shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa ba sa adawa da shirin gwamnati na sake duba rahoton shekarar 1992 matuƙar za a yi musu adalci.

Wannan layi ne

'Akwai waɗanda ba sa son zaman lafiya'

"Kafin harin da aka kai a Gora, mutanen gari sun zauna da Atyap da Fulani kuma aka yi yarjejeniyar zaman lafiya, har ma aka bai wa wasu Fulani tallafi amma ba a yi mako ɗaya ba sai ga shi an kai hari a garin," in ji Farfesa Lucius Bamaiyi, shugaban ƙungiyar Atyap Community Development Association (ACDA).

Lucius ya zargi Fulani da kai harin. Ya ƙara da cewa wannan ya sanyaya musu gwiwa a yaunƙurinsu na kawo zaman lafiya.

Shugaban ƙungiyar ta cigaban al'ummar Atyap ya ce abu ɗaya ne daga cikin shawarwarin da wancan rahoto na 1992 ya bayar ba a aiwatar ba, idan aka aiwatar da shi za a iya samun zaman lafiya.

"Muna jira mu ga abin da gwamnati za ta yi da shi domin ba mu san niyyarta ba," in ji shi.

Wannan layi ne