Kaduna: An saka dokar hana fita a Zangon Kataf kan rikicin ƙabilanci

Malam Nasir El-Rufai

Asalin hoton, Facebook/NasirEl-Rufai

Bayanan hoto, Rikicin ya samo asali ne kan wata gonar noma

Hukumomin tsaro a jihar Kaduna sun kafa dokar hana fita ta tsawon awa 24 a Masarautar Atiyep da ke Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf da Masarautar Chawai a Ƙaramar Hukumar Kauru.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis ta ce hakan ya biyo bayan wani rikici mai nasaba da ƙabilanci tsakanin Hausawa da 'yan ƙabilar Atiyep kan wata gona.

Rahotanni sun ce lamarin ya kai ga matasa rufe hanyoyin mota.

Kwamishinan harkokin tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan wanda ya je yankin, ya ce al'amura sun lafa.

Jihar Kaduna ta daɗe tana fusknatar rikicin ƙabilanci da na addini kasancewarta jiha mai ƙabilu daban-daban.

Kimanin mutum 55 ne 'yan sanda suka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wani rikicin na ƙabilanci a watan Oktoban 2018.

A lokuta da dama ba a hukunta waɗanda suke haddasa irin waɗannan rikice-rikice.