An nemi a ƙara ɗagewa ƙasashe matalauta lokacin biyan bashi

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Bankin Duniya ya yi gargaɗin cewa annobar korona na ƙara haddasa wata matsalar nauyin bashi ido rufe ga ƙasashe masu tasowa.
David Malpass ya yi wannan jawabi ne yayin wani taron ministocin kuɗi na ƙungiyar ƙasashen G20 ta hanyar intanet.
Ya ce nauyin basukan da ke kan ƙasashe matalauta na ƙaruwa zuwa wani mataki na tagayyara.
Don haka Mista David Malpass ya buƙaci ƙungiyar G20 ta ƙasashen da ke kan ganiyar bunƙasar tattalin arziƙi su tsawaita matakin jingine biyan basukan da suka amince da shi a baya da ƙarin shekara ɗaya.
Mai masaukin baƙi ministan harkokin Saudiyya, Mohammed Al Jadaan, ya ce annobar ta haifar da wani ƙalubale da ya karaɗe duniya.
A cewarsa ƙungiyar ƙasashen na aiki cikin hanzari don tunkarar tasirin da cutar ta haddasa wa tattalin arziƙi.
Annobar kobid-19 ta zama wata matsala mafi girma da ke fuskantar tattalin arziƙin duniya tun daga lokacin Gagarumar kiɗimewar duniya a shekarun 1930, in ji shi
"Don kai ɗauki game da haliin da aka shiga saboda wannan annoba, ƙasashen G20 na ɗaukar matakai namusamman kuma cikin hanzari wajen tunkarar al'amarin wannan annoba da kuma yadda ta yi tasiri cikin harkokin lafiya da na zamantakewa da ma tattalin arziƙi, ciki har da matakan daidaita harkoki da tsare-tsaren al'amuran kuɗi."

Asalin hoton, Getty Images
Ministan yYa kuma bayyana fatan ƙasashen za su amsa kiran Bankin Duniyar ta hanyar ci gaba da jingine biyan basukan:
"Mun fahimci tasirin abin da kuma rashin daidaiton shi kansa tasirin, da cutar kobid-19 ta haddasa kuma a gaskiya ta fi haifar da lahani ga ƙasashe masu rauni don haka muke son samar da tallafi.
Mun ɗauki matakai cikin hanzari kuma na tarihi a wannan ƙungiya ta G20 lokacin da muka bijiro da shirin dakatar da biyan basukan. Kuma ban ga abin da zai hana wannan yunƙuri ci gaba ba".











