Majalisar Najeriya ta amince wa Buhari cin bashin Naira tiriliyan 8.2

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Majalisar dattawan Najeriya ta amince wa Shugaba Muhammadu Buhari ya ciwo bashin Naira tiriliyan 8.2
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar ciyo bashin daga kasashen ketare na Naira tiriliyan tiriliyan 8,2, da Shugaba Buhari ya gabatar mata a bara.
Hakan dai ya biyo bayan wani zama na musamman ne da majalisar ta yi a ranar Alhamis.
Amincewar ta biyo bayan la'akarin da majalisar ta yi ne da rahoton kwamitinta a kan basussukan cikin gida da na waje.
Wasu 'yan majalisar dokokin dai sun bayyana damuwa, cewa bashin ya karkata ga amfanar wani bangare na Najeriya, yayin da wasu kuma suka yaba da irin ayyukan da za a yi da kudin da za a karbo bashi.
A karshen watan Nuwamban da ya gabata ne Shugaba Buhari ya nemi majalisar dattawan ta sake duba bukatar.
Ya kuma bukaci majalisar ta amince da shirin neman bashin daga kasashen ketare da gwamnatin tarayya ta gabatar mata tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018, don a samu kudaden da za su taimaka wajen aiwatar da manyan ayyukan da ke cikin kasafin kudin kasar na bana.







