Hukuncin kotun Birtaniya zai wa Najeriya illa - Emefiele

Hoton babban bankin Najeriya wato CBN kenan

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto, Babban Bankin Najeriya CBN ya ce lamarin zai iya shafar manufofin kudaden Najeriya

Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya mayar da martani bayan da wata kotun Birtaniya ta umarci Najeriya ta biya dala biliyan 9 ga wani karamin kamfani mai.

Mista Emefiele ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa gwamnatin kasar ba za ta amince da hukuncin kotun ba, wanda zai iya janyo wa asusun ajiyar kudaden waje na kasar cikas.

"Mun san cewa a cikin ilollin hukuncin dai, akwai na shafar manufofin kudaden kasar kuma shi ya sa CBN ke kokarin kare Najeriya da kuma kare asusun ajiyar kudadenta na waje," in ji shi.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana duba yiwuwar kama wasu jami'ai da take zargi da hannu a hukuncin kotun wanda ya bukaci sai ta biya wani kamfani tsabar kudi har dala biliyan 9, saboda saba yarjejeniya da suka kulla.

Kotun ta umarci gwamnatin Najeriya a ranar Juma'a da ta biya kamfanin Process & Industrial Developments Ltd (P&ID) wadannan makudan kudi ta hanyar kwace kadarorin gwamnatin kasar.

Tun farko a 2017 kotu ta bukaci kasar ta biya kamfanin kusan dala biliyan shida da rabi kafin yanzu kuma kotun London ta kara dala biliyan biyu da miliyan 400.

Jumullar kudin dai sun kai kwatankwacin kashi 20 cikin 100 na dukiyar da Najeriya ta ce ta tara a lalitar kudadenta na kasashen ketare wato dala biliyan 45.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, ya ce batun tsohuwar shari'ah ce da jami'an gwamnatocin baya suka gaza wajen daukaka kara, har damar ta wuce.

"Masu mulki a wancan zamani ba su daukaka kara ba har kofa ta toshe," in ji shi.

Ya kuma ce gwamnatin Buhari ta yi kokarin tunanin matakin da za ta dauka domin jinkirta aiwatar da hukuncin domin bude kofar ta daukaka kara, amma kotun a Ingila ta ce ba za ta bayar da wannan dama ba.

Ya zargi jami'an gwamnatin baya da yin sakaci kan abin da ya kira "hadin bakinsu don cutar da Najeriya har suka bari abu ya kasance haka."

Hakazalika ya ce duk da gwamnati za ta daukaka kara, amma abu na farko da za a yi shi ne duk wani wanda aka san da hannunsa a cikin wannan hadin baki don a cuci Najeriya tare da wani kamfani na kasar waje, gwamnati za ta sa a kamo su kuma za ta dauki mataki akansu.

Wata sanarwa a shafin intanet na kamfanin ta ce yarjejeniyar ta ba shi damar gina wata katafariyar masana'ntar gina sarrafa iskar gas wadda Najeriya za ta karba kyauta don bunkasa lantarki a kasar.

Amma kamfanin ya ce ya fuskanci karin kudin ruwa a kullum saboda rushewar yarjejeniyar, batun da lauyoyin gwamnatin Najeriya suka ce ya wuce hankali.