Su wane ne suka yi wa Ekweramadu a-ture-a-ture a Jamus?

Asalin hoton, Twitter
Shugabannin siyasa da kuma na mulki na ci gaba da yin Allah-wadai da harin da wasu da ake zargin 'yan kungiyar aware ta Biafra (IPOB) ne suka kaiwa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Ike Ekweramadu.
Shugaban majalisar Sanata Ahmed Lawal ya yi tur da yadda 'yan kungiyar suka "wulakanta" Sanata Ekweramadu a lokacin wani taro da aka gayyace shi a ranar Asabar a kasar Jamus, inda ya kwaci kansa da kyar.
A sanarwar da mai magana da yawunsa, Ola Awoniyi ya fitar, Ahmed Lawal ya ce "harin dabbanci da aka kai wa Sanata Ekweremadu a lokacin wani taro da aka gayyace shi ya ba da tasa fahimtar kan yadda za a ciyar da kabilar Igbo gaba, ya nuna irin rashin da'a da rashin wayewar al'ummarmu.
Abun a yi Allah-wadai da shi ne kuma abin takaici ne."
Daga karshe Sanata Ahmed ya nemi hukumomin kasar Jamus da su gaggauta nemo wadanda ke da hannu a aikata wannan mummunan al'amari.
Ita ma Daraktar Hukumar Kula da 'yan Najeriya Mazauna Kasashen waje, Abike Debiri-Erewa, a wata sanarwa, ta ce, "abin da ya faru da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan, Ike Ekweremadu abin kunya ne ga Najeriya, a idon duniya."
Ta kara da cewa "abin ya zubar da mutumcin 'yan kabilar Igbo kasancewar su ne 'yan Najeriya mafi rinjaye a kasar Jamus."
Me ya faru?
'Yan kabilar Igbo mazauna kasar Jamus ne dai suka gayyaci tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Sanata Ekweremadu da ya gabatar da kasida a taron ci gaba da kuma baje kolin al'adun kabilar Igbo a kasar Jamus.
Ana cikin wannan taro ne a birnin Nuremberg sai wasu "bata gari" da ake zargin 'ya'yan kungiyar da ke fafutukar ganin yankin kudu maso gabashin Najeriya ya balle daga kasar, wato IPOB, suka kutsa cikin taron suka far wa Sanata Ike Ekweremadu.
Wani bidiyo da shafin Sahara Reporters ya wallafa ya nuna yadda wasu mutane suka rinka kulle-kucciya da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ta Najeriya.
An ga wasu na dukan sa, inda wasu kuma ke jifan sa tare da kokarin cire masa riga, kafin daga bisani ya samu ya shiga mota ya tsere, inda ita kanta motar sai da aka bi ta ana duka.
Su dai 'yan wannan kungiya ta IPOB na zargin Sanata Ike Ekweremadu da hannu a "cibayan" da yankin kudu maso gabashin na Najeriya yake fuskanta musamman rashin yin katabus din manyan yankin wajen taimaka wa kungiyar ballewa.
Kungiyar IPOB, wacce aka haramta a kasar, ta dade tana sa kafar wando daya da jagororin yankin saboda kallon da suke yi musu na yi wa tafiyar kungiyar kafar ungulu.
Sai dai shugabannin yankin sun dade suna musanta irin wadannan zarge-zarge.











