Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kutse a WhatsApp: Yadda za ku kare shafukanku na sada zumunta daga kutse
- Marubuci, Daga Jimmy Blake
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Newsbeat
Kutsen da ake yawaita samu a shafukan sada zumunta kamar WhatsApp ya kai matakin da mutane a yanzu fatansu shi ne a wallafa labari mai jan hankali a kan faruwar hakan.
A lokuta da dama masu kutse na amfani da wata manhaja a wayar mutum da ke leken asiri ba tare da mutum ya ankara ba.
A baya-bayan nan ana yawaita kutse a shafukan sada zumuntar mutane musamman WhatsApp.
Ganin cewa wannan kutse na ci wa mutane tuwo a kwarya, ga wasu bayanan da za su iya taimakawa wajen kare sirrikanku.
Akwai lokutan da masana tsaro suka shaida wa shafin Facebook wanda ya mallaki WhastApp cewa; ''Masu kutse na aike sakonnin a wayoyin mutane wanda idan aka latsa shi kan ba su damar nadar bayanai
Sannan su kan yi amfani da wata manhaja wajen kiran mutum ta 'WhatsApp's call' domin samun damar kutsawa cikin waya.
Ko mutum bai dau kiran wayar ba, na'urarsu na iya shigar da wasu bayanai da za su ke leken asirin a cikin wayar mutum saboda rashin cikakken tsaro a jikin wayar.
Sannan wannan kira zai bace watakil ma ba za ka ankara cewa an kira ka ba, saboda masu kutsen na iya amfani da manhajarsu wajen goge wayar da suka maka.
Kashe waya da sake kunnata ko kashe ta kwata-kwata ba mafita ba ce.
A watan Mayun 2019, WhatsApp ya shawarci masu amfani da manhajar biliyan 1.5 su sabunta shi bayan bijiro da wasu matakan kare manhajar daga masu kutse.
Idan ka yi hakan akwai wata alamar ja da ke nunawa a rumbun manhajoji (ya danganta da irin wayar da ake amfani da ita ko Iphone ko Android) ba zai ci gaba da aiki kai tsaye ba.
Duk da cewa sakonnin WhatsApp ana ganinsu ne kawai tsakanin mai turawa da wanda aka turawa, sakon kutsen da ake aikewa na iya makalewa.
Akwai bukatar yawaita sabunta manhajarka saboda kullum bijiro da sabbin dabarun kutse ake yi.
Rage amfani da cloud
Kun san cewa sako na zama ne tsakanin wanda ya tura da inda aka tura shi - wannan shi ne babban abin da WhatsApp ya sanya a gaba.
Sai dai idan kai - ko abokanka - na adana tattaunawar da ka yi ta WhatsApp a wurare kamar Google Drive ko iCloud, to akwai matsala.
Saboda sakonnin da ka adana ba su da kariya, kai kadai da wanda kuka tattauna kawai ke da izinin ganin sakoninka, don haka duk mutumin da ke da damar kutsawa cloud din ka zai iya kwashe bayananka da duk wata tattaunawa.
Don haka idan mutum na bukatar sirri, to sai ya daina amfani da irin wadanan rumbun ajiyar.
Kana iya shiga cikin yanayi na mamaki da tambayar mafita - amma idan burinka shi ne kare wayarka da sirrikan ka kana iya zuwa wajen ''settings'' ka sauya yanayin adana tattaunawarka.
Sweet 2FA
Idan manhajarka tana da wannan dama (wanda WhatsAPP ke da ita), wasu matakai biyu na tsare sirri (2FA) na taimakawa sosai wajen kare bayananka.
Wannna kusan shi ne matakin kololuwa na tabbatar da cewa mutane sun kare bayyanansu daga masu kutsen da ba a ganinsu.
Da fari, Mutum zai shigar da sunan da ya ke amfani da shi da kuma makulinsa wato password.
Sannan, maimakon nan take a baka dama, za a bukaci tambarin dan 'yatsa ko muryarka ko kuma wasu lambobin da aka aika maka ta lambar waya alal misali.
Wasu lokutan kuma wasu tambayoyi ko bayananka za a bukata, kamar sunan abin da ka fi so ko maihaifiya da dai sauransu.
Sannan kuma ana iya sauya matakai biyu na kare wayarka ta ''settings'' din WhatsApp.
Zabin abin da ya fi dacewa da kai
WhatsApp da sauran manhajoji na da nasu hanyoyin kare bayanan sirri. A shiga Settings > Account > Privacy domin ganin yadda tsarin yake.
Daga nan kana iya zabin wanda zai ke ganin lokatun da ka hau ko ka sauka wato "last seen" da hotonka wato ''profile photo'' da kuma inda kake wato ''live location''.
Kana iya cire shi daga alamar da ke nuna an karanta sako, sai ta daina nuna alamar shudi idan ka karanta sakon mutum.
Kana kuma iya tsara yadda kake son manhajar ta yi aiki, da mutane da kake son suke ganin sakoninka.
Kar ka kasa bacci
Masu kutsen nan watakil sun fi ka sauri ko da kai lauya ne, ko mai fafutika ko dan rajin kare hakkin dan adam ko dan Jarida.
A cewar wani binciken kwamiti da ke kare 'yan jaridu, wadannan su ne mutanen da ake ganin sun fi fuskantar barazanar kutse.