Magu ya fita, Umar ya shiga: Abubuwan da suka faru a Najeriya makon jiya

Ibrahim Magu

Asalin hoton, EFCC

Lokacin karatu: Minti 4

Mako ya kare ya bar mu da waiwaye kan manyan abubuwan da suka faru a cikinsa.

Ga wasu muhimman batutuwa da suka faru a makon jiya daga ranar Litinin 6 ga watan Yuli zuwa Juma'a 10 ga watan Yuli a Najeriya a takaice.

Jami'an DSS sun 'tsare' shugaban EFCC Ibrahim Magu

A ranar Litinin ne kafofin watsa labaran Najeriya suka wayi gari da labarin cewa jami'an tsaro na farin kaya, DSS sun je kama shugaban riko na hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a kasar Ibrahim Magu.

Daga bisani, hukumar ta DSS da ma ta EFCC sun fitar da sanarwa daban-daban da suka ce gayyatarsa DSS ta yi.

Domin karanta karin bayani kan labarin, sai ku latsa nan.

Short presentational grey line

Fadar shugaban Najeriya ta dakatar da shugaban EFCC

Sai dai washegari, wato ranar Talata, wata majiya mai karfi da ta bukaci a sakaya ta daga Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar wa da BBC Hausa cewa an dakatar da shugaban na EFCC.

Majiyar ta kara da cewa Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba.

Domin karanta cikakken labarin, sai ku latsa nan.

An hana wakokin yabon Annabi a Kano sai da izinin gwamnati

"Tuni muka nemi gidajen rediyo a Kano su daina sanya irin wadannan wakoki har sai lokacin da muka bayar da izini"

Asalin hoton, Sanimaikatanga/Afakalla

Bayanan hoto, "Tuni muka nemi gidajen rediyo a Kano su daina sanya irin wadannan wakoki har sai lokacin da muka bayar da izini"

A ranar ta Talata hukumar tace fina-fanai da dab'i ta jihar Kano ta ce babu wani sha'iri da zai kara waka a jihar sai idan ta ba shi lasisi.

Shugaban hukumar Isma'il Muhammad Na'abba wanda aka fi sani da Afakallah ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC ta yi da shi.

Afakallah ya ce ganin yadda sha'irai ke wuce iyaka a lokuta da dama ya sa hukumar ta dauki wannan azama.

Talata ba ta kare ba sai da majalisar dokokin jihar Ondo ta aika wa Agboola Ajayi, mataimakin gwamnan jihar takardar shirin tsige shi daga kan mukaminsa.

'Yan majalisar sun ce za su dauki matakin ne sakamakon wasu laifuka da suka ce mataimakin gwamnan ya aikata.

Karin bayani a nan.

Short presentational grey line

'Ɗaliban Najeriya ba za su zana jarabawar WAEC ta 2020 ba

A ranar Laraba ne ministan ilimi na Najeriya Malam Adamu Adamu ya ce ɗaliban ƙasar waɗanda suke ajin ƙarshe na sakandire ba za su zana jarabawar WAEC ba saboda fargabar yaduwar cutar korona.

Ya sanar da hakan ga manema labarai bayan taron Majalisar Zartarwa na Tarayya.

Mun yi nazari abubuwa bakwai da daliban sakandare za su yi domin lashe jarrabawa. Latsa nan don karanta cikakken bayani.

Osinbajo ya musanta karɓar biliyoyin naira daga wurin Magu

Magu and Osinbajo

Asalin hoton, VP Twitter

A makon na jiya ne ofishin mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya musanta cewa ya karɓi naira biliyan hudu daga hannun Ibrahim Magu, shugaban hukumar EFCC da gwamnatin Najeriya ta dakatar domin biyan wata buƙata ta ƙashin kansa.

Wata sanarwa da Laolu Akande wanda shi ne kakakin mataimakin shugaban ƙasar ya fitar ta ƙaryata wasu labarai da aka wallafa a wasu jaridu na intanet da wasu saƙonnin Twitter da aka wallafa kan batun.

Hotunan gwaggwon birran da ba kasafai a kan gansu ba a Najeriya

A silverback Cross River gorilla

Asalin hoton, WCS Nigeria

A ranar Alhamis masu fafutukar kare muhalli sun ce a karon farko cikin shekaru an dauki hotunan wasu gwaggon birrai da ke rayuwa a wasu tsaunukan kudancin Najeriya.

Gwaggon birrai 300 ne kawai suka rage a dazukan jihar Cross River wanda ya sa suka zama cikin birrai irinsu na dawa da suka kusa karewa.

Amma kungiyar Wildlife Conservation Society mai rajin kare dabbobin dawa ta ce wannan labarin ya tabbatar da cewa dabbobin na hayayyafa sosai.

Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin 2020

A ranar Juma'a shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kudin kasar na 2020.

A kasafin kudin, wanda majalisun dokokin kasar suka yi wa kwaskwarima a watan jiya, za a kashe N10.8 a shekarar ta 2020.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A ranar ce kuma gwamnatin Najeriya ta nada Mohammed Umar a matsayin sabon mukaddashin shugaban EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

An nada Mohammed Umar a matsayin sabon mukaddashin shugaban EFCC ne bayan dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar.

sai ku latsa nan. don karanta sauran labarin.

Kazalika a ranar ta Juma'a aka sake bude filayen jiragen saman wasu jihohin kasar suka ci gaba da zirga-zirga, cikin har da filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar Kano.

Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne