Matsalar fyade: Hukunce-hukuncen fyade a addinin Musulunci

Pantami da Daurawa
Bayanan hoto, Malam addinin musulunci sun ce addinin ya tanadi hukuncin kisa kan fyade
    • Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Matsalar fyade ta jima tana ciwa al'umma tuwo a kwarya musamman a Najeriya. A 'yan kwanakin nan ana ta samun rahotannin karuwar cin zarafi da ke neman zama gama gari a cikin al'umma.

Fyade bai tsaya a kan manya ba ko 'yan mata, galibi a wannan zamanin an fi cin zarafin kananan yara da jarirai.

Wata kuri'ar jin ra'ayi da cibiyar Noipolls ta gudanar a watan Yulin 2019 ta nuna cewa a cikin mata uku a kan samu guda da ta fuskanci irin wannan cin zarafi kafin ta kai shekara 25 na rayuwarta.

Ba kasafai ake kai korafi ko kara kan fyade ba - wadanda aka yi wa wannan cin zarafi da'yan uwansu ko dangi na fargabar fitowa su yi magana saboda tsoron tsangwama da kyama daga sauran al'umma.

Short presentational grey line

Hukunci kan Fyade

An jima ana muhawara kan irin hukunci da ya kamata a rinka yankewa ko a dauka kan mutumin da aka samu da laifin fyade.

Babu wani tsayayyen hukuncin da dokokin Najeriya suka tanada a kan fyade, dokin kuwa kowace jihar tana da nata dokokin da suka tanadi hukuncin dauri kan wanda aka samu da laifin fyade.

Tsawon shekarun da za a daure mai laifin fyade sun kama daga shekara 14 a wasu jihohin, zuwa daurin rai da dai, wanda shi ne mafi yawa.

Pantami
Min Of Comm
Matuƙar an yi amfani da ƙarfi da barazana kamar ta makami, to wannan hukuncinsa na cikin Suratul Ma'idah Aya Ta 33.
Dr Isah Pantami
Malamin Addinin Musulunci a Najeriya

Sannan da dama daga jihohin sun tanadi cewa za a ba wa wacce aka yi wa fyade diyyar daidai sadakin irin wacce aka yi wa fyaden.

Short presentational grey line

Me Musulunci ya tanadar?

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr. Isa Ali Pantami ya ce akwai bukatar shigar da hukunce-hukuncen addini cikin dokokin yaki da fyaɗe, tun da a cewarsa addini ya yi magana a kansu.

"Idan fyade babu amfani da ƙarfi, babu barazana ga ran mace ko ga mutuncinta, to ana ɗaukar wannan al'amari a matsayin zina ne kamar yadda ya zo cikin suratul Annur," in ji Pantami.

Bayanan bidiyo, Dole a rika hukunta masu fyade- Sheikh Aminu Daurawa

Sai dai ya ce matuƙar an yi amfani da ƙarfi da barazana kamar ta makami, to wannan hukuncinsa na cikin suratul Ma'idah.

Dr. Pantami ya kuma ce waɗannan dokoki ne na Allah, kuma al'ummomin da suka kwatanta aiki da su, sun zauna lafiya.

Shi ma Sheikh Ibrahim Daurawa fitacen malamin addini ne da ke cewa fyade mumunan laifi ne a addinin Musulunci kuma ana iya yi wa mace ko namji.

Hukunce-hukuncen fyade sun kasu kashi 4 kamar yadda ya zo a cikin kundin yanke hukunci wanda malamai suka ba da fatawarsa a kasar Saudiya, in ji Daurawa.

Short presentational grey line

"Idan ya zama wanda aka yi wa fyaden mace ce babba ko karama sannan wanda aka yiwa fyaden na da aure ko babu aure, sannan namiji ne ko mace akwai abubuwan da ake duba wa.

"Haka kuma Idan mutum namiji ya yi wa mace fyade ana duba a ina ya yi mata fyaden, gidansa taje ko kuma shine yaje gidanta, sannan a wurin aiki ne ko kan hanya, sai a lura da yanayin da abin ya faru".

Malam Daurawa
Daurawa Facebook
Idan aka yi wa karamar yarinya fyade ko da ba a yi amfani da makami ba, to hukuncin wanda ya yi kisa ne.
Sheikh Aminu Daurawa
Malamin Islama a Najeriya

Yadda hukuncin yake - Daga Daurawa

  • Ana duba idan ya yi amfani da makami ko karfi, Saboda haka wanda ya yi wa mace fyade ta hanyar amfani da makami hukuncinsu guda da wanda ya yi fashi da makami, ma'ana hukucinsa kisa kai tsaye
  • Idan ya kasance mace ce mai girma kuma akwai laifinta a wannan bangaren to hukuncin zina ne ya hau kan wanda ya yi fyaden, hukuncin zina kuwa dama idan yana da aure to za a kashe shi, idan kuma bai taba aure ba to za a yi masa bulala 100 da daurin shekara guda da kuma tarar dala dubu 80 (kwatankwacin Naira miliyan 31) kamar yadda aka kayyade a yanzu.
  • Idan karamar yarinya aka yi wa fyade, malamai sun yi fatawar cewa hukuncinsa na kisa ne, idan kuma diyya za a karba to kwatankwacin ta kisa za a karba, domin kuwa ya lalata ta, idan kuwa dama mutum ya lalata wa mace mutuncinta ko ita ta lalatawa namiji to diyyarsa daidai take da ta rai - wanda a yanzu aka kiyasta akan naira miliyan 66 ko rakumi 100 ko Saniya 200 ko rago 2,000 ko dirhami 12,000
  • Idan kuma namiji aka yi wa fyade to hukuncin kisa ne saboda kai tsaye ya zama luwadi wanda kuma aka yi wa za a kare masa mutuncinsa da biya masa kudin kare lafiyarsa.
  • Idan kuwa karamar yarinya ce ko da ba a yi amfani da makami ba hukuncin na kisa ne.
  • Idan mace da amincewarta ta je inda ta san za a yi mata fyade to ita ma za a mata hukunci.
Wannan layi ne

Fyade a baya-baya nan

  • An tsinci gawar wata dalibar jami'a, Uwavera Omozuwa da ake zargin an yi mata fyade sanna aka fasa mata kai aka jefar da ita a cikin coci, yanzu haka ana tsare da wanda ake zargi
  • Wasu kartan maza sun shafe wata biyu suna yi wa wata yarinya 'yar shekara 12 fyade a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya; ana tsare da maza 11 da ake zargi
  • Ana zargin gungun maza sun yi wa Barakat Bello fyade a Jihar Oyo; har yanzu babu wanda aka kama
  • An kuma samu wata 'yar shekara 17 da ita ma gungun maza suka yiwa fyade a jihar Ekiti; an cafke mutum biyu.
  • An tsinci gawar yarinyar a wani masallaci da ke unguwar Kurmin Mashi da ke Kaduna, lamarin ya tayar da hankalin jama'a da dama
  • An yi wa wata yarinya 'yar wata uku fyade a jihar Nasarawa; an gurfanar da wani matshi a kotu bisa zarginsa da yi mata fyade.
Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Sharhi, Umaymah Sani Abdulmumin

A Najeriya an sha zargin cewa mutane da ka yi wa fyade na fargabar kai kara saboda tunanin cewa jami'an tsaro ba lallai su bi musu hakkinsu ba, sai dai mutum ya yi ta kashe kudi ana kai komo, abinda yake sa gaibin mutane suna sarewa da fitar da rai cewa ba lallai fannin shari'a ya kwato musu 'yancinsu ba.

Matsalar fyade da cin zarafin mata dai sake girma take, a baya-bayan nan ma sai da babban sufetan 'ƴan sandan kasar ya ce daga watan Janairu zuwa Mayu na wannan shekarar an samu rahotannin fyaɗe da 717 a fadin kasar.

Masana harkokin shari'a kamar Barista Bulama Bukarti na ganin daga matsalolin da ake fuskanta, akwai dogon lokacin da 'yan sanda ke dauka suna bincike, da kuma tsarin yadda kotunan kasar musamman masu bin kundin penal code ke tafi da al'amura.

Bulama ya ce da jihohin da suke aiwatar da tsarin musulunci za su ringa kai shari'ar fyade kotunan shari'a, da an fi saukin tabbatar da laifi ko kuma kore shi cikin kankanen lokaci.

"A kotun dake bin tsarin kundin panel code, dole ne a kawo shaidu kan cewa an yo fyade, amma a kotun shari'ar musulunci za a nemi wanda ake zargi ya rantse da Alkur'ani kan cewa bai aikata ba," in ji Audu Bulama.

Wannan layi ne