WAEC: Abubuwa bakwai da daliban sakandare za su yi domin lashe jarrabawa

Asalin hoton, AFP
A dalilin annobar korona da ta addabi daukacin kasashen duniya, a rufe makarantu wanda yasa aka dakatar da karatun da dalibai ke yi a dukkan matakai na ilimi tun daga na firamare zuwa na sakandare, har zuwa na jami'a.
A Najeriya, gwamnatin tarayya ta rufe dukkan makarantun kasar daga ranar 26 ga watan Maris na 2020, matakin da ya shafi makarantun gwamnatin da na masu zaman kansu.
Rufe makarantun yayi mummunan tasiri ga karatun dukkan daliban, ganin cewa an shafe fiye da wata uku daliban na zaune a gida.
Amma a wasu jihohin Najeriya, an rika gudanar da koyarwar wasu darusa ta hanyar intanet, was kuma ta akwatin talabijn wanda ana iya cewa kokari ne da aka yi domin cike wagegen gibin da ya bayyana saboda rufe makarantun da aka yi.
Sai dai a makon jiya gwamnatin Najeriya ta sanar da bude makarantun kasar ga daliban da ke aji na karshe domin su sami damar rubuta jarabawarsu ta karshe.
Ga daliban da ke ajin na babbar makarantar sakandare, za su rubutar jarabar da hukumar shirya jarabawa ta yankin Afirka ta yamma ke shiryawa wadda aka fi sani da WAEC.
Abubuwa bakwai da dalibai ke bukata domin lashe jarabawa
BBC ta tuntubi Kabir Isma'il, wani malamin makarantar sakandare a Kaduna da ke arewacin Najeriya, inda ta tambaye shi abubuwa bakwai da dalibai ya kamata su fi mayar da hankali a kai domin samun nasara a jarabawar ta WAEC da ke karatowa, musamman a wannan lokaci da ke fama da annobar korona.

Asalin hoton, PA Media
1. A nemo tsofaffin takardun jarabawa
Tilas dalibai su nemo tsofaffin takardun jarabawa da aka yi amfani da su a shekarun baya domin za su zama matsashiya a garesu.
Wannan dabara ce babba domin akan maimaita yawancin tambayoyin da ake yi wa dalibai daga shekara zuwa shekara.
2. Mayar da hankali kan karatu
Ya kamata dalibai su mayar da hankali wajen yin karatu ganin cewa sun shafe watanni suna zaune a gida. Masu iya magana na cewa "Kowa ya bar gida, gida ya bar shi".
Saboda haka ya dace dalibai su ajiye dukan abubuwan da za su kawar da hankulansu daga karatu a gefe guda idan suna son samun nasara a jarabawar mai zuwa.
3. A bi sahun manhajar karatu
Sai kuma batun bin manhajar karatu. Wannan ma abu ne mai muhimmanci kwarai da gaske ganin cewa a kowace shekara ma'aikatar ilimi na tsara manhajar karatu ne domin cimma muradun daliban da za su rubuta jarabawa kamar wannan.
4. Littattafai
Yawancin dalibai ba su da littatafan da ake koyar da darussa wato textbooks. Wannan babban kuskure ne.
Rashin wadannan litattafai kamai zuwa gona ne a manta da fartanya. Duka bin da za a koyar a ciki aji idan ka duba za ka same shi a cikin litattafai.
Dalibin da ke da wayo zai iya samun garabasa idan ya mallaki dukkan litattafan darussan da ya ke son rubuta jarabawa akai.
5. A nemi taimakon masana
Sai kuma batun neman taimako daga kwararrun malamai ko abokansu dalibai.
Lallai akwai bukatar dalibai su nemi malaman da suka san darussan sosai domin su nuna mu su wuraren da ya kamata su fi mayar da hankali da kuma dabarun da za su yi amfani da su wajen amsa tambayoyin da za su ci karo da su cikin jarabawar da za su tunkara nan ba da dadewa ba.
Sai dai ya kamata a mayar da hankali wajen bayar da tazara da tsaftace kansu domin kiyaye kamuwa da cutar korona.
6. A tara tunani wuri guda
Ana kuma son dalibin da zai rubuta jarabawa kamar ta WAEC ya tara tunaninsa wuri guda. Kada ya karaya domin yaga aikin na da yawa.
Idan ya gaya wa kansa cewa zai iya samun nasarar cin jarabawar, sai ya ga hakan ya faru. Wannan sirrin bai tsaya ga jarabawa kawai ba, har ma ga sauran bangarori na rayuwar da Adam.
7. Samun isasshen hutu
A karshe akwai kuma dabarar amfani da yawancin lokacin da mutum ke da shi wajen yin karatu da hutawa.
Kamar yadda kowa ya sani ne, dan Adam na bukatar hutu bayan ya yi aiki. Karatu irin wannan na da cin zuciya da kuma gajiyarwa domin ana amfani da kwakwalwa ne.
Idan ba a samar wa jiki hutu ba, to jiki zai gaza a daidai lokacin da kae bukatarsa ya aiwatar da abin da aka sanya a gaba.











