Coronavirus a Kano: Shin Ganduje na shirin sake bude makarantu?

Ganduje

Asalin hoton, Kano govt

Gwamnatin jihar Kano ta musanta cewa za ta fara shirye-shiryen bude makarantu da aka rufe saboda tsoron yaduwar cutar korona, sabanin rahotannin da wasu kafofin watsa labarai suka bayar cewa gwamnatin ta kafa wani kwamiti domin nazari kan sake bude makarantun.

Kwamishinan ilimi a jihar Mohammad Sunusi Sa'id Kiru ne ya shaida wa BBC Hausa haka a yayin wata hira da ya yi da Khalifa Shehu Dokaji a ranar Litinin.

Kwamishinan ya ce abin da suka sani shi ne sun kafa wani kwarya-kwaryar kwamiti da zai bayar da shawara kan kundin da ma'aikatar ilimin Najeriya ta turo jihohin kasar 36 don nazari kafin bude makarantun kasar.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kungiyar malaman makarantun Islamiyya a jihar ke ci gaba da kiraye-kirayen gwamnati da ta bude makarantun islamiyyu, bayan amincewa da bude gidajen kallon kwallo da kasuwani da gwamnatin ta yi.

Kungiyar makarantun islmaiyyar dai ta yi barazanar fita zanga-zanga idan har ba a amsa bukatar tasu ba.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron yadda tattaunawarsu ta kasance:

Bayanan sautiHira da kwamishinan ilimi na Kano Mohammad Sunusi Sa'id Kiru

Karin labarai masu alaka: