Coronavirus a Kano: Za a fara bin gida-gida don yin gwajin cutar

Gwamnan Kano Ganduje

Asalin hoton, FACEBOOK/ABBA ANWAR

Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce za ta fara bi gida-gida domin yi wa al'ummar jihar gwajin cutar korona.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana ranar Alhamis hakan a yayin wata ganawa da manema labarai don bayar da bayanai a kan halin da ake ciki a yaki da cutar corona a jahar.

Ganduje ya ce duk da matakan da gwamnatin jahar ke dauka kan dakile yaduwar cutar korona, yin gwajin don gano masu dauke da cutar zai taimaka wajen samun nasarar kawo karshen cutar a kan lokaci.

Gwamnan ya ce, kasancewar akwai kananan hukumomi uku da suka fi yawan masu cutar a jihar, shi ya sa aka dauki wannan mataki na bin gida-gida don gwaji musamman a kananan hukumomin da abin ya fi kamari.

Ganduje ya ce kananan hukumomin su ne Nasarawa da Tarauni da kuma Municipal.

Kwamishinan yada labarai na jihar ta Kano, Malam Muhammad Garba, ya shaida wa BBC cewa adadin mutanen da ke kai kansu asibiti domin a gwada su a Kano ya yi kasa shi ya sa gwamnati ta ga ya dace a fara wannan gwaji ta hanyar bin gida-gida.

Muhammad Garba ya ce: "Za a fara bin gida-gida don gwajin ne daga karamar hukumar Nasarawa saboda itace tafi yawan masu wannan cuta a cikin kananan hukumomi 44 da jahar ke da su. Kafin fara wannan gwaji, za a fara ba wa ma'aikatan kiwon lafiya horo na musamman a kan yadda za su gudanar da wannan gwaji na bin gida-gida".

Kwamishinan ya kara da cewa: "Idan aka fara gwajin gida-gidan a kananan hukumomin da cutar tafi yaduwa, to suma sauran kananan hukumomin jahar za a rinka tsintar wadanda za a yiwa gwajin,don ba za a barsu a baya ba".

Wannan mataki da gwamnatin jahar ta dauka na zuwa ne kwanaki bayan gwamnatin ta bayar da umarnin bude kasuwanni da wuraren ibadu a ranakun Laraba da Jumma'a da kuma Lahadi bayan an shafe tsawon lokaci suna rufe saboda cutar korona.

Karin bayani kan coronavirus