Coronavirus a Kano: Ganduje ya fusata alarammomi kan yi wa almajirai dirar mikiya

Ganduje

Asalin hoton, Facebook/Abba Anwar

Kungiyar mahaddata Kur'ani ta Najeriya ta bayyana bacin rai kan ci gaba da yin dirar mikiya kan makarantun allo cikin dare ana kwashe almajirai tare da killace su a Kano.

Gwamnati ta ce tana ci gaba da 'killace almajirai fiye da 2000 a wasu sassan jihar, a yunkurinta na dakile yaduwar annobar korona'. Ta ce shawarar kwashe almajiran ta daukacin jihohin arewa ne.

Malaman makarantun allon dai na nuna cewa gwamnati ba ta yi shawara ko tuntuba da su ba, ballantana ma a yi batun ba su wani wa'adi kafin fara wannan aiki na kwashe almajiran.

Yayin zantawa ta wayar tarho da BBC, babban magatakardan kungiyar, Gwani Sanusi Abubakar ya ce suna kira na fahimta ga Gwamna Ganduje da lallai-lallai ya dakatar... kuma ya yi gyara sannan a saki almajiran da ake tsare da su.

Ya ce sun ziyarci daya daga cibiyoyin da ake tsare da irin wadannan almajirai a garin Zakirai cikin jihar Kano. A cewarsa: "Mutum ne dai kamar yana tsare amma yana dan watayawa".

"Shi shugaban wurin ya fada mana yawan yara su 480 ne aka kawo. Kuma yara ne da aka samu suna karatu a nan Kano amma sun fito ne daga jihohin Kebbi da Sokoto da Zamfara da kuma Katsina," in ji shi.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce akwai yarjejeniya da suka cimma tsakanin gwamnonin jihohin arewa wadda ke tabbatar da ganin kowacce jiha ta mayar da almajiranta zuwa jihohinsu na asali.

Kuma tuni jihar Kano ta kwashe daruruwan almajiran, inda ta mayar da su zuwa jihohinsu a manyan motocin safa-safa da kuma bas-bas.

Wasu dai na zargin yanayin da ake kwashe almajiran, ba ya ba da damar tabbatar da tazara a lokacin tafiyar, don haka abu ne mai yiwuwa kananan yaran su iya yada cutar korona a tsakaninsu matukar wani a cikinsu na da ita.

Shi dai a cewar Gwani Sanusi yanayin da almajiran da suka gani ke ciki (a cibiyoyin killacewar) ba yabo ne ba fallasa. "Gaskiya wadannan da muka gani lafiyarsu kalau musamman shi babban jami'in cibiyar yana kula da su".

Ya ce an hada su da jami'an da ke kula da su wadanda ko da an samu wani cikin almajiran ba shi da lafiya su ne sukan dauke su don zuwa neman magani.

"Sun kuma kai mu kicin inda ake dafa musu abinci, sun nuna mana taliya da shinkafa kuma da kunu da ake yi." Ya kara da cewa duk da haka yaran sun nuna abincin ba ya isarsu.

Ya ce tun da suna da kungiyoyi da shugabanni, kamata ya yi gwamnati ta kira su don sanar da su yadda suke so a yi.

Malamin ya ce tun da gyara ake nema, su masu karbar gyara ne, don haka ya kamata a zauna don tattaunawa da su.

"Yarjejeniyar da cimma ce ta ba da dama ga gwamnatin jihar Kano, ta ci gaba da wannan tsari duk da shigowar annobar korona," in ji kwamishina Tsanyawa.

Almajirci

Asalin hoton, Getty Images

Ya ce suna da cibiyoyi guda uku da ake tsugunnar da almajiran da ba 'yan asalin jihar Kano ba, inda ake kula da su, kuma ana ba su abinci tare da kula da lafiyarsu.

Ya kara da cewa: "Jami'an lafiya suna zuwa su duba su a kai a kai. Haka kuma gwamnatinsu ta fito da tsarin gwada almajiran don tantance ko sun kamu da cutar korona.

"Gabanin sallamarsu su tafi gida, idan sakamakon gwajinsu ya fito an tabbatar ba su da cutar korona," kwamishinan ya ce.

Jihohi irinsu Kaduna da Jigawa sun yi zargin cewa gwajin da suka yi wa almajiran da jihar Kano ta mayar musu, na nuna cewa wasunsu na dauke da cutar.

Lamarin dai ya janyo kiraye-kiraye a kasar cewa gwamnatocin su dakatar da wannan shiri na kwashe almajiran cikin irin wannan yanayi mai hatsari.

Yayin da su ma kwararru a fannin lafiya a Nijeriya suka nuna fargabar cewa yunkurin na iya haddasa fantsamar annobar da ake fama da ita maimakon dakile yaduwarta a tsakanin al'umma.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus