'Almajirai 19 daga Kano ne suka kara yawan masu korona a Kaduna'

Asalin hoton, @GovKaduna
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir Elrufa'i ya ce sun samu karin mutum 19 masu dauke da cutar korona, al'amarin da ya kara yawan adadin masu cutar a jihar daga 9 zuwa 25.
Elrufa'i wanda ya wallafa wannan bayani a shafinsa na Twitter, ya ce an yi wa almajirai 40 gwaji, inda sakamakon 19 daga cikinsu ya nuna suna dauke da cutar ta korona.
Gwamna Elrufa'i ya kuma kara da cewa yanzu ta tabbata shige da fice da ake yi wa jihar tasa ne ke janyo karuwa masu cutar a Kaduna, inda ya ja hankalin jami'an tsaro da su ci gaba da sanya ido kan duk masu shiga birnin ta barauniyar hanya.
Ko a makon da ya gabata ma sai da gwamnan ya sanar cewa sun samu biyar daga cikin almajiran da aka mayar wa jihar tasa daga Kano masu dauke da cutar.
A kokarin dakile bazuwar cutar korona a birnin Kano ne dai ya sa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya fito da shirin mayar da almajirai jihohinsu na asali.
Masana harkar lafiya da dama sun soki shirin bisa dogaro da cewa hakan ka iya fantsama cutar a wasu jihohin da ba su da ita.
Tun a ranar 22 ga watan Afrilu ne gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 suka sanar da rufe dukkanin makarantun tsangaya kuma babu jimawa gwamnatin Kano ta fara mayar da su jihohinsu na asali.
Jihar Kano ta mayar da yaran jihohinsu na asali da suka hada da Katsina da Kaduna.
Akalla yara miliyan tara ne aka yi hasashen za a mayar da su gaban iyayensu sakamakon annobar korona.











