Coronavirus: Elrufa'i ya tsawaita dokar hana fita a Kaduna

Asalin hoton, @GovKaduna
Gwamnatin Kaduna da ke arewacin Najeriya ta tsawaita dokar hana fita tsawon wata daya a yunkurinta na dakile bazuwar cutar korona a jihar.
Gwamnatin jihar ta sanar a shafinta na Twitter cewa gwanna Malam Nasir Elrufa'i ya tsawaita dokar ne bisa shawarwarin da kwamitin jihar kan cutar korona ya bayar karkashin jagorancin Mataimakiyar gwamnan jihar, Dr Hadiza Balarabe.
Gwamnatin Kaduna kuma ta ce za ta tilasta amfani da abin rufe fuska saboda muhimmancinsa wajen rage yaduwar cutar tsakanin mutane da kuma kare lafiyar jama'a.
A ranar 26 ga watan Maris ne gwamnatin Kaduna ta fara sanar da dokar hana fita a jihar, kuma yanzu Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki ranar Lahadi 26 ga Afrilu.
Gwamnatin ta umurci jama'a su zauna a gidajensu sannan wuraren ibada da shaguna da wuraren bukukuwa da kasuwanni za su kasance a rufe.
Sanarwar ta ce za a hukunta duk wanda ya saba dokar ta hanyar tara da kuma kwace motarsa.
Sannan gwamnatin Kaduna ta ce yadda cutar ke bazuwa, za ta rufe kofofin shiga jihar, kuma duk wanda aka kama ya shiga ko ya ratsa za a bukaci ya koma inda ya fito ko kuma a killace shi na tsawon mako biyu.


Gwamna El-Rufai shi ne mutum na farko da cutar ta kama a jiharsa ta Kaduna, amma ya sanar da warkewa daga cutar ranar Laraba 22 ga watan Afrilu bayan ya kamu da korona ranar 28 ga watan Maris.
Zuwa yanzu mutum 10 hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa NCDC ta ce sun kamu da cutar korona a jihar Kaduna.











