Coronavirus: Gwamnan Kaduna Nasir Elrufa'i ya ce ya warke

Gwamnan Kaduna Nasir El Rufa'i

Asalin hoton, @GovKaduna

Bayanan hoto, Elrufa'i ya sanar da yana dauke da cutar korona a ranar 28 ga watan Maris
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Elrufa'i ya ce ya warke daga cutar korona bayan shafe kusan wata ɗaya yana killace.

Malam Nasir Elrufa'i ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce "Ina farin cikin sanar da ku a yau cewa bayan kusan makonni hudu ina karbar magani, yanzu na warke daga cutar bayan gwaje-gwaje guda biyu da aka gudanar sun nuna ba na ɗauke da cutar.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Gwamna El-Rufai ya sanar da cewa ya kamu da cutar korona ne ranar 28 ga watan Maris.

Shi ne mutum na farko da cutar ta kama a jiharsa ta Kaduna, yayin da yanzu mutum 9 hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ce sun kamu da cutar a Kaduna.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Mataimakiyar gwamnan jihar, Dr Hadiza Balarabe ce ta ci gaba da tafiyar da harakokin gwamnatin Kaduna.

Bayan sanar da labarin warkewarsa, gwamnan ya godewa mataimakiyarsa Dr Hadiza Balarabe kan jajircewarta wajen tafiyar da harakokin gwamnati a lokuttan da yake jinyar cutar korona.

Shafin Twitter na gwamnatin Kaduna ya wallafa cewa bayan sallamar gwamna Elrufa'i, nan take ne kuma ja jagoranci tattaunawa da kwamitin da ke yaƙi da cutar korona a jihar, kafin kuma ya shiga taron kungiyar gwamnoni ta intanet.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne