Da gaske jami'an DSS sun tsare shugaban EFCC Ibrahim Magu?

Magu

Asalin hoton, TWITTER/@EFCC

Rahotanni daga Najeriya na cewa jami'an tsaron DSS a kasar sun 'gayyaci' shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu domin yi masa tambayoyi.

Kafofin watsa labaran kasar sun nuna cewa jami'an tsaro sun je ofishin hukumar inda suka bukaci Mr Magu ya bi su.

Sai dai wata sanarwa da DSS ta fitar ranar Litinin ta ce ba kama Mr Magu ta yi ba.

Kakakin DSS Peter Afunanya ya ce: "DSS tana so ta shaida wa al'umma cewa ba ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban EFCC ba, kamar yadda wasu kafafen watsa labarai suka bayar da rahoto."

Rahotanni dai sun nuna cewa an tafi da Mr Magu fadar shugaban kasa inda ake zargin zai gurfana a gaban wani kwamiti da shugaban kasa ya kafa don duba zarge-zargen da ake yi masa na almundahana.

An hana 'yan jarida shiga

Kafafen yada labaran kasar sun ruwito cewa an hana 'yan jarida shiga wajen kwamitin da ya gurfanar da Mista Magun a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an umarci 'yan jaridar da suka je don daukar rahoto da misalin 3:20 na yamma cikin ''nutsuwa'' cewa su bar wajen.

Short presentational grey line

Zarge-zarge da 'yar tsama da Abubakar Malami

Wannan lmari dai na zuwan bayan wasu zarge-zarge da ake y wa Magu na mallakar wasu kadarori hudu da kuma boye kudade a kasar wajen ta hannun wasu.

A baya-bayan nan jaridun najeriya sun ruwaito cewa Ministan Shari'a Abubakar Malami ya nemi Shugaba Buhari ya sauke Magu kan zarinsa da karkatar da kudaden da aka kwato.

Sai dai Magu ya musanta zargin yana mai cewa tuggun siyasa.

Fabrairun 2018

Ko a watan Fabrairun 2018 ma gwamnatin Najeriya ta tuhumi Ibrahim Magu da babban lauyan kasar Mr. Festus Keyamo.

An tuhumi mutanen biyu ne saboda tuhuma kan cin hanci da suke yi wa shugaban kotun kula da da'ar ma'aikata, Mr. Danladi Yakubu Umar.

Kafar watsa labarai ta The PRNigeria ta ce ta samu wasika biyu na tuhuma da aka aike wa Magu and Keyamo.

A cikin wasikun, wadanda aka aike musu ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar 2018, an bukaci Ibrahim Magu ya aika da amsarsa ga ministan shari'a kafin ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu.

Wannan layi ne