Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Naya Rivera: Yadda tauraruwar fina-finai ta halaka a cikin ruwa amma ɗanta ya tsira
An bayyana mutuwar tauraruwar fim ɗin Glee Naya Rivera bayan an ceto ɗanta ɗan shekara huɗu wanda aka gani shi kaɗai a cikin kwale-kwale a kogin Southern California da ke Amurka, a cewar jami'ai.
Tauraruwar mai shekara 33 ta karɓi aron kwale-kwale ranar Laraba da rana a wurin shaƙatawar Lake Piru, da ke Los Angeles, a cewar ofishin shugaban 'yan sandan yankin Ventura.
Sanarwar da ofishin ya fitar ta ƙara da cewa ana yunƙurin "nemo da ɗauko" tauraruwar. Babu wata alama da ke nuna cewa akwai hannun wani a game da mutuwarta.
Rivera ta shahara a wasan kwaikwayon Glee inda ake kiranta da suna Santana Lopez.
An riƙa sanya wasan kwaikwayon na barkwanci a kafar watsa labarai ta Fox daga 2009 zuwa 2015.
Me aka sani game da hatsarin kwale-kwalen?
Wani kwale-kwale ne ya hango ɗan Rivera awa uku bayan ta karɓi aron kwale-kwale, a cewar jaridar CBS Los Angeles, wacce ta ambato ofishin shugaban 'yan sandan yankin.
fishin ya kara da cewa ɗan nata ya gaya wa masu bincke cewa shi da mahaifiyarsa suna ninƙaya - amma ba ta dawo cikin kwale-kwalen ba.
Daga bisani aka sanar cewa Naya Rivera ce a cikin kwale-kwalen, a cewar wani mazaunin Los Angeles.
Shugaban 'yan sandan ya ce za a rufe wurin shakatawar a yayin da ake ci gaba da nemanta ranar Alhamis, wanda kwararrun masu kurme suke yi.
Ranar Alhamis, babban jami'in 'yan sanda na Ventura Chris Dyer oya ce hukumomi sun mayar da hankali wurin gano da dauko ta.