Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar Fyade: Yadda aka yi wa yarinya fyade aka jefar da gawarta a masallaci a Kaduna
Hukumomi a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da cewa yarinyar nan da aka ga gawarta a wani masallaci a makon jiya fyade ne aka yi mata.
Kwamishinar kula da harkokin mata da walwalar jama'a ta jihar ta shaida wa BBC cewa rahoton binciken da ta samu ya nuna cewa fyade ne aka yi mata kuma ta ce yanzu haka jami'an tsaro sun dukufa don gano wanda ya yi mata fyaden.
A ranar Juma'a ne aka tsinci gawar yarinyar a wani masallaci da ke unguwar Kurmin Mashi, lamarin da ya tayar da hankalin jama'a da dama.
Bayanan da BBC ta samu sun ce lamarin ya afku ne a unguwar Kurmin Mashi da ke yankin karamar hukumar Kaduna Ta Kudu.
Wani Mazaunin unguwar ne ya fara ganin gawar yarinyar yashe a cikin masallacin inda nan take mutane suka taru suna nuna takaicinsu da kuma mamaki.
Bayan da 'yan sanda suka isa wurin ne sai aka nemi iyayenta. Malam Yau Abdullahi shi ne mahaifin yarinyar 'yar shekara shida.
''Tana cikin gida tana wasa ba a ankara ba sai aka ga ba ta nan. Na dawo daga masallaci sai aka ce min ba a ganta ba. To wallahi har yanzu ba mu san yaya aka yi ta bace daga cikin sauran yara da suke wasa tsakanin cikin gida da kofar gida ba.
Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta kaddamar da bincike don gano wanda ya aikata fyaden. Hajiya Hafsat Baba ita ce kwamishinar kula da jin dadin jama'a ta jihar, ta kuma za su gabatar da rahoton bincikensu ga gwamna.
''Har yanzu ba a kai ga kama kowa ba amma jami;an tsaro suna kokarinsu sosai.
''Al'amarin nan na ba mu tsoro don lamarin fyade karuwa yake yi a Kaduna kowace yara.''
Haka ma BBC ta ji ta bakin daya daga cikin mutanen da suka yi uwa suka yi makarbiya wajen ganin an kai gawar yarinyar asibiti don gudanar da bincike.
Farfesa Hauwa Yusuf mamba ce a kungiyar yaki da cin zarafin al'umma a jihar Kaduna, kuma ita ce ta ce tilas sai iyaye sun tashi tsaye wajen kula da 'ya'yansu.
A jihar Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya ma rundunar 'yan sanda ta kama mahaifin wata budurwa da badakala.
Kamen dai ya biyo bayan kai karar mutumin dan shekara 61 da yin lalata da 'yarsa tun tana karama.
Matsalar fyaɗe da cin zarafin mata na ci gaba da karuwa a Najeriya, a baya-bayan nan ma sai da babban sufetan 'ƴan sandan kasar ya ce daga watan Janairu zuwa Mayu na wannan shekarar an samu rahotannin fyaɗe har ɗari bakwai da goma sha bakwai (717) a fadin kasar.