Najeriya: Me ya sa maza suke yi wa mata fyade a kasar?

Fyaɗe wata matsala ce da ke ƙara kamari a Najeriya musamman yadda ake cin zarafin mata da ƙananan yara ta hanyar fyaden.

A ranar Litinin rundunar ƴan sandan jahar Jigawa da ke arewacin a Najeriya ta tabbatar da kama mutum 11 da ake zarginsu da yi wa wata yarinya mai shekaru 12 fyade.

Ƴan sandan a Jigawa sun ce sun kama mutanen ne bayan wani koke da suka samu daga kasuwar Limawa da ke ƙaramar hukumar Dutse, inda aka zargi wani mutum mai kimanin shekaru 57 da yunkurin cin zarafin wata yarinya.

Wannan kuma na zuwa a dai-dai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kisan wata dalibar jami'a mai shekaru 22 da ake zargin ta rasa ranta sanadin fyade a wata majami'a da ke kusa da jami'ar Benin a jahar Edo.

Ana dai danganta karuwar matsalar ga wasu dalilai da suka hada da rashin dokoki masu karfi na hukunta masu aikata fyaden.

Ko da yake hukumomi a kasar na cewa suna iya bakin ƙoƙarinsu akan matsalar kuma a watannin da suka gabata ne hukumar yaƙi da safarar mutane a Najeriya, NAPTIP, ta ce tana tsara kundin rijistar masu aikata fyade da ta kaddamar a watan Disamba.

Hukumar ta ce rijistar za ta taimaka wajen daƙile aikata fyaɗe da hana wa waɗanda aka samu da laifin cin zarafi ta hanyar lalata da suka haɗa da yin fyade tsallakawa zuwa sassan ƙasar domin sake aikata laifin.

Wata ƙididdigar da kungiyar kare hakkin mata ta Women At Risk International Foundation ta fitar, ya nuna ana cin zarafin dubban mata a kowacce rana a Najeriya.

Fyaɗe dai yanzu, babbar matsala ce da ke neman zama ruwan dare a ƙasar, lamarin da ke ci wa iyaye da hukumomi tuwo a ƙwarya.

A kan samu yanayin da makusanci ke yi wa ƴaƴan da ke da dangantaka da shi fyade, ko jami'an tsaro su yi amfani da ƙarfi ko kuma tsoho ya yi wa yarinya fyaɗe.

Akwai rahotanni da dama daga yankuna daban-daban na Najeriya da ke nuna yadda mahaifi ke yi wa 'yarsa ta cikinsa fyaɗe, ko ɗan shekara 70 ya yi wa ƴar shekara bakwai fyaɗe ko kuma yadda samari kan yi wa ƴan mata fyaɗe.

Masana kiwon lafiya sun ce fyaɗe na tattare da hatsari ga rayuwar matan da aka yi wa fyade domin za su iya kamuwa da cuttuka kamar ƙanjamau da kuma ɗaukar ciki.

Me ke janyo fyaɗe?

Tsananin bukatar yin jima'i - Likitoci sun ce wannan matsala na faruwa ne sakamakon ciwon ƙwaƙwalwar da ke damun mutanen da ke aikata fyaɗe.

Dr Attahiru Muhammad Bello, wani likitan ƙwaƙwalwa ne a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Adamawa, kuma ya shaida wa BBC cewa matsalar gagaruma ce.

"Yawancin masu yi wa ƙananan yara fyaɗe suna fama da cutar da a Turance ake kira paraphilia, wato wata jarabar matuƙar bukatar yin jima'i, ko da kuwa da wani abu kamar ƙarfe ne ko kuma ƙananan yara."

Ya ce a kasashen da aka ci gaba ana sanya musu ido idan aka ga suna nuna irin wannan ɗabi'u tun suna yara ta yadda za a riƙa yi musu magani tare da da ba su shawarwari.

Taɓin ƙwaƙwalwa - Dr Shehu Saleh shugaban asibitin kula da masu lalular ƙwaƙwala da ke garin Kware a jihar sokoto ya ce matsalar taɓin ƙwaƙwalwa na daga cikin dalilan da ke sa wasu su aikata fyaɗe musamman wadanda ba za su iya bambance abu mai kyau da marar kyau ba, kamar waɗanda ke aikata sata ko fashi da makami.

"Duk za su iya aikata fyaɗe saboda ba su san cewa laifi ne suka aikata ba, saboda ƙwaƙwalwarsu ta juye."

Sai dai Likitan ya ce yawancin masu aikata fyaɗe dama ce suka samu tsakaninsu da waɗanda suke yi wa fyaɗen da kuma mugun halin da ke ransu.

Ya ce akwai hanyoyi da dama da mutum zai bi ya biya bukatarsa ta samun gamsuwa amma saboda mugun halin da ke ransu ke sa su aikata yin fyaɗe.

Likitan ya ce fyaɗe na iya jefa yaran da aka yi wa cikin damuwa kan mugun abin da aka aikata masu, wanda zai iya shafar ƙwaƙwalwarsu.

"Babban matsalar fyade shi ne yaran da aka yi wa fyaden, yana janyo masu taɓin hankali har ta kai su ma suna yi wa wasu fyaden," in shi Dr Shehu Saleh.

'Tsattsauran hukunci'

Wasu dai na ganin rashin hukunta wadanda aka samu da laifin fyaɗe ne yake sanya al'amarin yake kara ta'azzara.

Uwar gidan shugaban Naijeriya, Aisha Buhari, ta taba bayyana damuwa game yadda ake sassauta wa masu yi wa mata fyade a Najeriya, tana mai kira da a tsaurara dokokin hukunta wadanda aka samu da laifin.

Aisha Buhari ta yi kiran ne a watan Disamban 2017 bayan wata shari'ar da aka yi a jihar Kano inda aka ci wani mutum tarar naira dubu goma kacal bayan an same shi da laifin yi wa wata jaririya fyade.

Uwar gidan shugaba kasar dai tana son a gyara dokokin ƙasar ta yadda duk wanda aka samu da laifin cin zarafin mata da kananan yara ba zai sake yin lafin ba.

Kungiyoyi masu zaman kansu dai na dora alhakin habakar matsalar akan rashin doka mai karfi na hukunta wadanda ke aikata laifin fyade a Najeriya.

Malaman addini a nasu ɓangaren na ganin ana samun yawaitar fyaɗe musammam a kan kananan yara ne saboda neman abin duniya.

Dr Abdullahi Pakistan, wani Malamin addinin musulunci a birnin Kano ya ce abu uku ne ke haddasa wannan matsala:

"Tsananin neman duniya, inda za ka ga boka ko matsafi ya bukaci mutum ya aikata fyade ko ya cire agarar wani, ko kuma ya tono gawa domin biyan bukatunsa.

Sai kuma shaye-shaye da ke batar da hanakalin mutane ta yadda ba sa sanin abin da suke aikatawa, da kuma tasowa cikin rashin tarbiyya.

"Mutane ba su san abin da ake kira tausayi ba. Duk mutumin da bai samu tausayi ba, ba zai tausayawa wani ba," a cewar babban malamin Islamar.

Malamin ya ƙara da cewa ya kamata hukumomi su rika yanke tsattsauran hukuncin kan duk mutumin da aka samu da laifin fyaɗe, sannan a gefe ɗaya kuma iyaye su duƙufa wajen yi wa ƴaƴansu tarbiyya baya ga wa'azi da Malamai za su mayar da hankali wajen yi wa al'umma kan illar wannan matsala.

Da alama dai wannan batu zai ci gaba da jan hankalin mutane a Najeriya, kuma zai ci gaba da kasancewa babban ƙalubale ga ƴan ƙasar da ma hukumomi, wadanda ake buƙatar su ɗauki matakai ƙwarara domin shawo kansa.

Tsoron tsangwamna

Galibi ana ganin rashin fitowa a kai kuka ga hukumomi da kuma karancin hukunci mai tsanani a kan fyade ne ke taimakawa aukuwar matsalar.

Masana suna alakanta rashin fallasa zancen fyade ga dalilai na addini da al'ada da kuma rashin son kunyata a cikin al'umma.

Sau da yawa a kan samu iyaye maza da suke yi wa ƴaƴansu ƴan mata fyade amma saboda gudun abin kunya, sai a lullube maganar.

A mafi yawancin lokaci, da zarar an ɗaga irin wannan maganar, abin da ke biyo baya shi ne kyama daga wurin al'umma.

A wani lokaci a akan samu yanayin da yarinya ba za ta samu manemi ba sakamakon fuskantar matsalar fyade duk kuwa da cewa ba a son ranta aka yi mata fyaden ba.

Wasu na ganin girman matsalar fyaɗe da illolinsa ga makomar mace ya kai girman da ya kamata duk wadda aka yi wa ta fito ta bayyana domin hukunta waɗanda suka aikata mummunan laifin wanda shi zai kawo ƙarshen matsalar.

Sannan zartar da hukunci mai tsauri zai zama izina ga masu aikata fyaɗe.

Mene ne fyade?

Dakta Nu'uman Habib, masanin halayyar dan Adam ne a Jami'ar Bayero da ke Kano kuma a cewarsa, "fyaɗe yana nufin haike wa mata, wani sa'in ma har maza ba tare da izininsu ba, ba tare da sahalewarsu ba, ba tare da yardarsu ba."

Dakta Nu'uman ya ce tasirin fyaɗe na da girma musamman a rayuwar yara, don kuwa ya kan daɗe a kwakwalwarsu kuma ya jefa su cikin damuwa da tsoro da rashin yarda da amincewa.

"Duk wanda suka haɗu da shi sai su yi tsammanin mai irin wannan halayyar ne. Kuma damuwar takan daɗe tare da su a cikin kwakwalawarsu kusan ta sa ma su sukurkuce", a cewarsa.

Sai dai bisa alama jama'a ba su gane haka ba, don kuwa ba a cika tattauna batutuwan da suka shafi fyade ba, bare a bai wa wanda a ka yi wa taimakon da ya dace.

Idan aka yi wa wata ko wani fyaɗe, shi da iyalansa sukan zage dantse su tabbatar mutane ba su sani ba. Wannan ba ya rasa nasaba da ƙyama da ake nuna wa waɗanda aka yi wa fyaɗe da iyalansu.

Kuma wannan yana hana jami'an tsaro yin aikinsu yadda ya kamata, musamman ta fannin bincike da yanke hukunci ga wanda ya aikata laifin.

Abin da ya fi dacewa

Hajiya Rabia Ibrahim, shugabar wata ƙungiya mai zaman kanta da ke ayyukan kula da mata da kananan yara da marayu a jihar Kaduna a Najeriya, mai suna ARRADA ta shawarci jama'a musamman iyaye kan yadda ya kamata su kula da kai komon 'ya'yansu.

  • Ya kamata iyaye musamman mata su sanya ido kan masu kula da ƴaƴansu, misali direba ko kuma mai aiki.
  • Iyaye su kula sosai da mutanen da ƴaƴansu suke matuƙar shakuwa da su misali kawunni ko gwaggo ko anti da dai sauransu.
  • Kula da masu yawan yi wa yara wasa ko kuma ba su kyaututtuka.
  • Ka da iyaye su rinka korar ƴaƴaansu da su je su yi wasa domin ƙyale su don su shakata.
  • Iyaye mata su rinka duba al'aurar yaƴansu musamman idan suka zo suna kuka saboda ba su san komi ba.