Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar fyaɗe: An gurfanar da wanda ya yi lalata da jaririya ‘yar wata uku a kotun Nasarawa
Gargadi: Akwai kalamai masu tayar da hankali a wannan labarin:
An gurfanar da wani mutum da ake zargi da yi wa jaririya 'yar wata uku fyade a kotu da ke jihar Nasarawa ta Najeriya.
Hukumar tsaron farin kaya da kare al'umma ta Najeriya wato NSCDC, wacce ta kama mutumin mai suna Ahmadu Yaro ranar Litinin da ta wuce, ta ce za ta tabbatar an yi masa hukuncin da ya dace.
Kwamandan hukumar a jihar ta Nasarawa Dr Muhammad Gidado Fari ne ya bayyana wa BBC hakan ranar Laraba da safe.
A cewarsa, kotun ta amince su ci gaba da rike mutumin a hannunsu har lokacin da za ta sake zama saboda annobar korona.
"Mutumin ya je gidan su jaririyar ne wata uku da suka gabata inda take kwance tsakanin mahaifanta amma ya dauke ta ya yi mata fyade. Lamarin ya yi muni sosai domin har hanjinta sai da ya fito.
Da farko an kai ta asibitin Dalhatu Arab da ke jihar Nasarawa, amma da batun ya gagare su an tafi da ita asibitin Jami'ar Jos inda ake sa ran yi mata tiyata sau tara", in ji Dr Muhammad Gidado Fari.
Ya kara da cewa yanzu an sallame su daga asibiti amma za su koma ranar 29 ga watan Yuni.
Batun fyade yana ci gaba da tayar da hankalin jama'a a Najeriya, inda ake samun labaran wannan mummunar dabi'a daga sassa daban-daban na kasar.
A farkon watan nan, rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta ce ta kama wani mutum bisa zargin yi wa mata 40 fyade, ciki har da mai shekara 80.
A makwabciyarta, wato jihar Jigawa, wata yarinya mai shekara 12 ta shaida wa 'yan sanda cewa wasu mutum 12 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.
A jihar Edo da ke kudancin kasar, an kashe wata ɗaliba ƴar jami'a bayan zargin yi mata fyade a coci.
Masu fafutuka na ganin ya kamata a rika kashe ko dandaƙe duk mutumin da aka samu da laifin yin fyade, ko da yake majalaisar wakilan kasar ta yi watsi da wannan ra'ayi.