Lazarus Chakwera: Jagoran adawa na Malawi ya doke Shugaba Peter Mutharika a zaɓe

Opposition Malawi Congress Party leader Lazarus Chakwera addresses supporters (file picture)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lazarus Chakwera ya samu nasarar lashe zaben ne bayan kotu ta soke zaben farko na 2019

Jagoran adawa na Malawi Lazarus Chakwera ya lashe zaben shugaban ƙasa zagaye na biyu da aka gudanar.

Ya doke shugaba mai ci Peter Mutharika da kashi 58.57 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaben da aka gudanar ranar Talata, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar ranar Asabar

A watan Fabrairu, Kotun kundin tsarin mulki ta Malawi ta doke nasarar da shugaba Mutharika ya samu a zaben watan Mayun 2019, inda ta ce an yi maguɗi a zaben.

Zaɓen zagaye na biyu da aka gudanar makon nan ya raba kan al'ummar ƙasar.

Karo na biyu kenan a Afirka ana soke zaɓen shugaban kasa kan zargin maguɗi bayan Kenya a 2017

Bayan sanar da sakamakon zaɓen a ranar Asabar, Mista Chakwera ya ce nasarar da ya samu "nasara ce ga dimokuraɗiyya da tabbatar da adalci": yana mai cewa "zuciyata na cike da farin ciki"

Magoya bayansa sun mamaye titunan Lilongwe, babban birnin Malawi, suna wasan wuta da yayata gari da odar mota.

line

Kalubalen da ke gaban sabon shugaban na Malawi

Daga Editan Afirka Will Ross

Wannan wani lokaci ne mai matukar muhimmanci a tarihin siyasar Malawi, kuma hakan ya tabbatar da cewa ƙarfin ikon shugaban ƙasa ya kasa tasiri ga ɓangaren shari'ar ƙasar da kuma masu jefa kuri'a.

An taɓa soke zaben shugaban ƙasa a Kenya shekaru biyar da suka gabata - Amma samun ɗan adawa ya yi galaba zaben a zagaye na biyu wani abu ne da ba a saba gani ba.

Malawi incumbent President Peter Mutharika

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba mai barin gado Peter Mutharika ya yi Allah waddai da sakamakon zaben

Kotun kundin tsarin mulki ce ta soke zaben Peter Mutharika a zaben da aka gudanar a bara bayan hujjoji da suka nuna zaɓen na cike da kura-kurai, kafin daga baya ya garzaya kotun ƙoli don ƙalubalantar hukuncin.

Alƙalan kotun ƙoli sun fuskanci matsin lamba wanda ya sa suka jajirce. Kuma yanzu mutanen Malawi sun juya masa baya.

Yanzu Mista Mutharika na kukan cewa an zalunce shi kuma zai ƙalubalanci zaɓen, amma yanzu mutanen Malawi sun zaɓi Lazarus Chakwera matsayin sabon shugabansu.

Sabon shugaban wanda malamin kirista ne, kalubalen farko da ke gabansa shi ne farfaɗo da ƙasar da ta yi fama da rikicin siyasa.

line

A yayin da ya ke jawabi kafin bayyana sakamakon zaɓen, Mista Mutharika duk da ya ce "zaɓe ne da ba za a yarda da shi ba amma kyakkyawan fatansa shi ne ciyar da ƙasa gaba ba koma baya ba."

Me ya sa aka sake zaɓe?

A 2019 ne kotun kundin tsarin mulki ta buƙaci a sake gudanar da zabe bayan ta soke zaɓen farko da ta ce an yi maguɗi.

A zaben farko shugaba Mutharika ne ya yi nasara inda ya sha da ƙyar da kasa da kuri'u 159,000.

Mista Chakwera, wanda ya zo na biyu a zaben, ya ƙalubalanci sakamakon inda ya ce an yi aringizo.

Presentational white space

Rashin tabbas game da sakamakon ya jefa ƙasar cikin zaman dar-dar wanda ya haifar da arangama tsakanin magoya bayan ƴan adawa da kuma ƴan sanda.

A woman casts her ballot during the presidential elections in Lilongwe on June 23, 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An gudanar da zaben kasar zagaye na biyu cikin kwanciyar hankali

Wane neLazarus Chakwera?

Jagoran adawa ne, kuma tsohon malamin kirista, wanda ke jagorantar jam'iyyar Congress Party (MCP).

An haife shi a Lilongwe inda ya fito a gidan manoma, ya yi alkawalin ƙarin albashi ga ma'aikata daga cikin sauye sauyen da ya ce zai kawo.

Mr Chakwera shi ya jagoranci hadakar jam'iyyu guda tara da ake kira Tonse Alliance, kuma ya samu goyon bayan tsohuwar shugabar kasar Joyce Banda da kuma mataimakin shugaban kasa Saulos Chilima, a matsayin abokin takararsa.

Mr Chilima - wanda ya zo na uku a zaben 2019 - na hannun dama ne ga shugaba Mutharika, kafin su raba gari.