Peter Mutharika: Shugaban Malawi ya ki amincewa da shan kaye a zabe

Shugaban Malawi Peter Mutharika

Asalin hoton, AFP

Duk da cewa Hukukamr Zaben Malawi (MEC) ba ta kai ga bayyana sakamakon karshe daga zagaye na biyu na zaben shugaban kasa ba, alamun farko-farko na nuna cewa shugaba mai ci Peter Mutharika yana bayan babban mai kalubalntarsa Lazarus Chakwera.

Mr Mutharika ya ce babu wanda ya lashe zaben kuma babu wanda ya fadi, sannan ya ki amincewa da shan kaye.

A cewar mataimakinsa, Atupele Muluzi, wanda ya ce Muthrika ne ya tura shi ya yi wa manema labarai jawabi, shugaban yana kiran magoya bayansa su yi watsi da rahotannin da ke cewa ya fadi a zaben, yana mai cewa dole ne a jira hukumar zabe ta bayyana sakamakon a hukumance.

Atupele Muluzi wanda ɗa ne ga tsohon shugaban kasar, Bakili Muluzi kuma jagoran wata karamar jam'iyyar hamayya, the United Democratic Front (UDF) wacce a baya ta taba yin kawance da jam'iyya mai mulki ta Muthrika Democratic Progressive Party (DPP).

Wani ɗan takarar, Muluzi ya yi ikirarin cewa kimanin masu sa ido 15 da jam'iyyun DPP da UDF suka tura yankin da 'yan hamayya suke da karfi sun yi batan dabo, kuma ana fargabar cewa sun mutu bayan magoya bayan jam'iyyar hamayya sun kai musu farmaki.

Sakamako daga duka yankuna 28, wanda jami'ai da wakilan jam'iyyu suka sanyawa hannu a matakin yankuna, sun nuna cewa Shugaba Muthrika yana bayan Lazarus Chakwera - wanda ya jagoranci babbar jam'iyyar hamayya ta Malawi Congress Party kuma ya wakilci hadakar Tonse Alliance wacce ta hada jam'iyyun hamayya tara.