Lassa 'tana kisa fiye da cutar korona' a jihar Bauchi

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin lafiya a matakin farko a jihar Bauchin Najeriya sun ce suna cikin tsaka mai wuya sakamakon yadda zazzabin lassa ke yaduwa a wasu yankunan Jihar cikin gaggawa.
Wannan yanayi na zuwa ne a lokacin da kusan daukacin jahohin Najeriya hankali ya karkata kacokan wajen takaddama da cutar korona.
Hukumomin sun ce daga farkon wannan shekara ta 2020 zuwa yanzu cutar ta lassa ta kashe mutane 41 a jahar, yayin da cutar korona ta kashe mutum uku kawai tun lokacin bullarta zuwa yanzu.
Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko a jahar ta Bauchi Dakta Ridwan Muhammed ya shaidawa BBC cewa sun fahimci cewa masu dauke da cutar ba sa zuwa asibiti ko kula da tsaftar jikinsu.
Ya ce dama a kowacce shekara akan samu bular cutar a Bauchi, sai dai a wannan karon yanayin ya yi tsanani saboda masu kula da marasa lafiya na ta mutuwa.
''Sai ka iske kowa daga kan miji da uwa da 'ya da dansu kowa na mutuwa saboda ba su da masaniya kan abin da ke kashe su wasu ma cewa suke iska ce ko mayu''
Likitan ya ce cutar na yaduwa ne tsakanin mutane idan babu kula da tsafta kamar wanke hannu musamman idan anyi mu'amala da mai dauke da cutar.
Ya ce yanzu haka akwai wanda ke kwance a asibiti ana wanke masa koda saboda kamun da cutar ta yi masa.
''Duk wayanda ke mutuwa, kodar ke daina aiki sai kaga suna zub da jini wanda hakan shi ne alamomin cutar''
Mutane na boye mutuwa gashi ana samun karin mace-mace da ke da nasaba da wannan cuta.

Asalin hoton, AUSCAPE

Dakta Ridwan ya ce gwamnati ta bada damar a soma feshi a yankunan da aka fi samun mace-mace da bin gida-gida don kawo karshen wannan cuta da ke kisa sannu a hankali a yankunan Bauchi.
Sannan ya ce za su soma feshin ne daga yankin Toro har rijiyoyi za a bi a yi feshi.
Zazzabin lassa dai ta sha kisa a Najeriya sai dai da alama a wannan lokaci saboda fama da ake da annobar korona ba a bata wani muhimmanci.
Ko a farkon wannan shekara sai da aka samu barkewarta a kasar, har aka fida sanarwar mutuwar mutane akalla mutum 41 bayan samu sama da 100 dauke da cutar a sassan Najeriya.
A shekarar 2016 ma jihar Kano ta kasance cikin jihohin kasar da suka yi fama da cutar ta zazzabin Lassa kafin daga baya a shawo kanta.
Masana lafiya dai sun bayyana cewa zazzabin Lassa ba shi da magani, don haka ne hukumomi suke wayar da kai kan hanyoyin da za a bi domin kariya daga kamuwa da cutar mai saurin kisa.












