Mece ce cutar Lassa, kuma wadanne matakai ne na kariya?

bera

Asalin hoton, Auscape

A ranar Laraba ne gwamnatin Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Lassa a jihar.

Tuni dai hukumomin lafiya a jihar suka ce sun dukufa wajen shawo kan barkewar annobar zazzabin Lassan.

Wasu majiyoyi a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano sun tabbatar da cewa gwaje-gwajen da aka yi sun nuna cewa zazzabin Lassa ne ake fama da shi a jihar.

Akalla jami'an lafiya biyu ne suka mutu a asibitin, yayin da wani kuma ke kwance yana jinya.

Baya ga jihar Kano ma akwai wasu jihohin kasar da ke fama da annobar zazzabin na Lassa.

Short presentational grey line

Mene ne Zazzabin Lassa?

Dakta Nasiru Sani Gwarzo, masani ne kan harkar lafiya, kuma a hirarsa da BBC ya ce cutar zazzabin Lassa wata kwayar cuta ce ta 'Virus', mai haddasa tsananin zazzabi mai bullar jini a jiki, wanda ake kira a Turance - 'viral heamorraghic fever'.

Ita wannan cuta tana zuwa wata sa'in da wasu alamomi da ba ayyanannu ba kamar mura da mashako da samun matsalar numfashi.

Asalin cutar ana samun ta ne daga wurin daga nau'in wasu beraye da ake kira 'multimammet rats' a Turance.

Ita wannan nau'in beran ana samunsu ne a dazuka ko wajen gari ko kuma a gonaki.

Tana da nonuwa a jere irin na kariya ba irin berayen gida ba. To amma idan suka kamu da cutar, suna yada wa berayen gida.

Wannan layi ne

'Hanyoyin kamuwa da cutar Lassa'

Yayin da mutum ya shaki kurar fitsarin wannan beran ko bahayansu ko ya taba wani danshi da ke fita daga jikin, ko kuma mutum ya ci wannan bera, sai ya kamu da wannan cutar.

Hakazalika idan akwai bera ko berayen da ke dauke da wannan cuta a cikin dakin ajiya wato 'store' sai masu sharar wurin suka shaki kurar, suna iya kamuwa da wannan cutar.

Tana shiga ta huhu da baki da makogwaro ko hanci. Haka kuma idan mutum ya kamu da cutar, wani ma ya zo ya taba shi, zai iya kamuwa shi ma da cutar.

Ana daukar cutar ne ta hanyar shakar iska mai dauke da cutar ko taba gumin jikin mutum ko fitsarinsa ko jininsa da dai wani danshi da zai fito a jikin mai dauke da ita.

Ba a cika ganin alamominsu da wuri ba, har sai cutar ta yi barna.

Ma'aikatan jinya ko na kiwon lafiya sun fi shiga hadarin kamuwa da wannan cuta saboda mu'amala da masu shi.

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirar BBC Hausa da Dakta Nasiru Sani Gwarzo:

Bayanan sautiBayanin Dr Nasiru Sani Gwarzo kan Cutar Lassa

'Illolin cutar Lassa ga jikin dan adam'

Cutar Lassa na da illoli da daman gaske ga jikin dan adam. Duk wani wuri da ke da abinda ake kira a Turance 'Epithelial Lining' yana cutarwa.

Yana shiga kwakwalwa da koda da duk wani sashe na jikin dan adam. Illar cutar ya fi muni ga magudanan jini.

Wannan layi ne

'Matakan kariya'

Idan mutum ya kamu da cutar Lassa, 'yan uwansa su yi hanzarin sanar da hukuma ta asibiti. Idan a gida yake, akwai dabarun da za a bi a dauke shi a kai shi asibiti ta hanyar da ba za a kamu da cutar ba.

Ana sa rigar kariya da safar hannu masu inganci kamar irin wadda ake amfani da ita idan mutum ya kamu da cutar 'ebola'.

Sai kuma a dora mai cutar a kan magani. Idan suka fara shan magani da wuri, sukan rayu su warke ba tare da cutar ta yi musu barna ba.

Danginsa su guji nacin cewa sai sun kai masa ziyara a asibiti, domin a nan ake dauko cutar.

Idan kuma an yi rashin sa'a ba a rayu ba rai ya yi halinsa, to nan ma, ka da danginsa suce sai dole an ba su gawar sun tafi da ita gida.

Domin kuwa ko ruwan wankar gawar kanta idan ta taba mutum, zai iya kamuwa da cutar Lassa.

Wannan layi ne