Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: BUA ya bayar da gudunmowar naira biliyan daya
Kamfanin BUA Group ya sanar da bayar da gudunmowar naira bilyan daya ga gwamnatin Najeriya domin yaki da cutar coronavirus.
Mai kamfanin na BUA Group, Abdul Samad Rabiu wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa baya ga kudin, kamfanin ya kuma bayar da kayan aiki da suka hada da injina da na'urorin gwaji da sauransu ga jihohi 9 na kasar.
Jihohin dai su ne Lagos da Kano da Adamawa da Edo da Kwara da Rivers da Abia da Akwa Ibom da kuma Sokoto.
Abdul Samad ya kuma ja hankalin sauran kamfanoni masu zaman kansu da su tallafa wa gwamnati wajen ganin an dakile wannan annoba, inda ya kara da cewa kamfanin nasa zai bayar da naira bilyan dayar ne ta hanyar babban bankin Najeriya.
Wannan tallafin dai na zuwa ne kwana daya bayan da shugaba Muhammaud Buhari ya amince da fitar da N15bn domin yakar annobar, inda jihar Legas ta samu N10bn sannan aka bai wa hukumar NCDC mai yaki da cutar, N5bn.