Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sama da mutum 1,000 na dauke da Covid-19 a Afirka
Mutanen da ke dauke da annobar coronavirus a nahiyar Afirka sun zarce mutum 1,000 a karshen wannan makon kamar yadda hukumar da ke yaki da cututtuka ta nahiyar ta bayyana.
A halin yanzu akwai masu dauke da cutar kusan 1,198 a nahiyar in ji hukumar.
Kasar Uganda ta bayyana mutum na farko da ya kamu da cutar a kasar inda kasar ta ce wani fasinja ne da ya zo daga Dubai.
Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan shugaban kasar ya bayyana matakai daban-daban da kasar ta dauka na hana tarurruka da kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen sama.
A kasar Rwanda kuma, gwamnatin kasar ta bayyana cewa za a kara wa'adin matakan da ta dauka na dakatar da hada-hada a kasar da kusan makonni biyu.
A Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo kuwa, an samu mutuwa ta farko sakamakon cutar coronavirus inda wani likita ne ya mutu bayan ya kwaso cutar daga kasar Faransa.
Hukumar da ke kula da yaduwar cututtuka a nahiyar Afirka ta bayyana cewa mutum 108 sun warke daga cutar.