Coronavirus: Ministocina na aiki ba dare ba rana – Buhari

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana da "cikakken kwarin gwiwa" kan ministoci da jami'an lafiyar kasar a yakin da Najeriya ke yi da cutar coronavirus.

Wannan magana ta shugaban na zuwa ne yayin da wasu ke sukarsa kan yadda ya yi gum da bakinsa a lokacin da sauran shugabannin duniya ke yi wa 'yan kasarsu bayani kan yadda suke yaki da cutar a kasashensu.

Tun bayan da coronavirus ta bulla Najeriya Buhari bai yi wa 'yan kasa bayani ba kan halin da ake ciki amma mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya bayyana dalilin da ya hana shi yi wa kasa bayani.

"Kare hakkin 'yan Najeriya na cikin kudirin wannan gwamnati," Buhari ya wallafa a Twiiter. "Muna da hukumar yaki da yaduwar cutuka ta NCDC da Ma'aikatar Lafiya da ke aiki ba dare ba rana."

Ya kara da cewa: "Ina da cikakken kwarin gwiwa kan ministocina da alhakin abin ya rataya a wuyansu da kwamiti na musamman da na kafa kwanan nan da kuma jami'an hukumar NCDC, wadanda suke bayar da bayanai a-kai-a-kai da kuma shawarwari."

Ba a bar 'yan Najeriya a baya ba

Kamar yadda aka saba, 'yan Najeriya kan tofa albarkacin bakinsu a kodayaushe a duk abin da ya shafi rayuwarsu.

Wani mai suna @person_pikin1 cewa ya yi: "Baba ka fiya jan kafa a komai."

Shi kuwa @Muhammad_M_Abba ya ce: "Wannan shugaba ka cancanci ka zama shugaban Najeriya na har abada idan da hali."

Wannan kuma cewa ya yi: "Mabiya miliyan 2.6 kawai gare ka (a Twitter). Ka fito ka yi wa 'yan kasa miliyan 180 bayani."