Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Italy: Dybala da Maldini sun kamu da Coronavirus
Dan kwallon Juventus da kuma Argentina Paulo Dybala ya kamu da cutar Coronavirus.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Dybala ya ce shi da buduwarsa duk suna dauke da cutar.
"Ni da Oriana muna da cutar, amma muna cikin yanayi me kyau" in ji Dybala mai shekara 26.
Shi ma tsohon kyaftin din Italiya, Paolo Maldini ya kamu da cutar.
Dybala ne dan kwallon Juve na uku da aka tabbatar ya kamu da Coronavirus bayan dan wasan baya Daniele Rugani da kuma Blaise Matuidi.
Tuni aka dakatar da gasar kwallon Italiya ta Serie A saboda cutar.