An dakatar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano

EFCC ta ce Danja ya sha cirar kudaden lokacin da shi kadai ne zai iya cewa ko an gudanar da ayyuka kafin biyan kudi

Asalin hoton, Kano asssembly

Bayanan hoto, EFCC ta ce Danja ya sha cirar kudaden lokacin da shi kadai ne zai iya cewa ko an gudanar da ayyuka kafin biyan kudi

Majalisar dokokin jihar Kano da ke Najeriya ta dakatar da 'ya'yanta biyar zuwa wata shida bayan an zarge su keta dokokin majalisar.

Shugaban majalisar, Abdulazeez Gafasa ne ya sanar da dakatar da Garba Ya'u Gwarmai da Labaran Audu Madari da Isyaku Ali Danja da Bello Muhammad da kuma Salisu Ahmad Gwangwazo

Ya ce sun dauki matakin ne saboda yunkurin da 'yan majalisar suka yi na dauke sandar majalisar a makon jiya.

'Yan majalisar dai sun yi yunkurin dauke sandar ne saboda zargin da suka yi cewa gwamnatin Abdullahi Ganduje ta hada baki da wasu 'yan majalisar domin yin amfani da majalisar wurin sauke Sarki Muhammadu Sanusi na II.

BBC ta yi yunkurin jin ta bakin dukkan bangarorin amma bata yi nasara ba.