Majalisar dokokin Kano ta kafa kwamitin binciken Sarki Muhammadu Sanusi II

Asalin hoton, Majeeda Studio
Majalisar dokokin jihar Kano a arewacin Najeriya ta kafa kwamiti domin binciken Sarki Muhammadu Sanusi II kan korafe-karafe biyu da aka gabatar mata.
Majalisar ta ce korafe-korafen sun hada da zargin Sarki Sanusi II da yin kalaman da basu dace da addinin Musulunci da al'ada ba.
A yayin zaman majalisar na ranar Laraba, shugaban majalisar ya shaida wa 'yan majalisa cewa ya karbi korafe-korafen ne daga wata Kungiyar Bunkasa Ilimi da Al'ada ta Kano da kuma wani mutum, Muhammad Mukhtar mazaunin karamar hukumar Gwale a ranar Litinin.
Sai dai bincike ya nuna ba a taba jin wata kungiya mai suna Kungiyar Bunkasa Ilimi da Al'ada ta Kano ba sai wannan lokaci.
Majalisar ta kafa kwamiti ne ranar Laraba karkashin dan majalisa Zubairu Hamza Masu, inda aka ba shi kwana bakwai ya gabatar da rahotonsa.
Shugaban majalisar ya ce masu korafe-korafen sun yi zargin cewa Sarkin Kano ya yi wasu abubuwa da suka saba mutuntaka da addini da al'adar mutanen Kano.
Amma bai fayyace abubuwan da Sarki Sanusi II ya yi ba wadanda suka saba addini da al'adun Kano.
Zubairu Masu ya ce masu korafin sun gabatar da faya-fayen CD da hotuna a matsayin shaida kan zargin da suka yi wa Sarkin.
Sai dai wasu 'yan majalisar sun kalubalanci matakin kafa kwamitin ba tare da yi musu cikakken bayani kan masu korafin ba.
Majalisar ta hau kujerer na-ki
Wasu 'yan jarida da suka halarci zaman majalisar sun ce dan majalisa mai wakiltar mazabar Dala, Lawal Usaini, ya nemi karin bayani kan korafin da shaidun da aka gabatarwa majalisar, amma shugaban majalisar ya hau kujerer na-ki inda.
Ya ce kwamitin zai duba dukkan bayanai da hujjojin da aka gabatar.
Ba wannan ne karon farko da majalisar take yunkurin gudanar da bincike kan Sarki Muhammadu Sanusi II ba tun da aka fara samun takun-saka tsakaninsa da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
A karon farko dai majalisar ta dakatar da binciken bayan shiga tsakani da wasu manya da suka hada da Alhaji Aliko Dangote suka yi.

Ita ma hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafen al'umma ta Kano ta fara wani sabon bincike kan zargin karkatar da kudade da ake yi wa Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi II.
Wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC cewa hukumar ta aike da takardar gayyata ga Sarkin na Kano a ranar Laraba.
Hukumar dai tana bukatar Sarkin ya bayyana ranar Alhamis a gabanta domin amsa tambayoyi kan yadda aka sayar da wasu filaye mallakin masarautar aka kuma karkatar da wasu miliyoyi naira.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce an gayyaci Sarkin ne bayan tambayoyi ga daya daga manyan 'yan majalisarsa, wanda ake zargi yana da hannu a badakalar karkatar da kudaden.
Hukumar ta karbar korafe-korafe ta kaddamar da bincike da dama kan masarautar Kano karkashin Sarki Muhammadu Sanusi II da kuma shi kansa Sarkin.
Binciken da hukumar ta yi sun hadar da na zargin yadda aka kashe wasu daruruwan miliyoyi naira wajen biyan kudin waya tun bayan hawan Sarkin Muhammadu Sanusi II karagar mulki, da bincike kan zargin yadda ake sayar da wasu filaye na gandun Sarki ba bisa ka'ida ba, da kuma bincike kan zargin sayar da filayen masarauta a unguwar Darmanawa da karkatar da kudin.
Ita dai masarautar Kano da Sarki Sanusi II sun sha musanta duk zarge-zargen.
Wasu dai na ganin duka binciken da majalisar da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi na da nasaba da siyasa musamman ganin rashin jituwar da ke tsakanin Sarkin na Kano da Gwamna Ganduje.

Asalin hoton, Muhd Kano emirate photography











