Trump ya ce a koma ga Allah kan Coronavirus

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar addu'o'i a kasa baki daya domin neman sauki daga annobar cutar coronavirus.
Shugaban ya roki Amurkawa da su dukufa wurin addu'o'i a duk inda suke.
"A duk inda kuke, na karfafi gwiwarku da ku mika lamuranku ga Allah da addu'o'i. Cikin sauki sai ku ga mun tsira tare," Trump ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Ya kara da cewa: "Cikin girmamawa, na ayyana Lahadi 15 ga watan Maris a matsayin Ranar Addu'o'i ta Kasa. Kasarmu, a tarihi, ta sha mika lamuranta ga Allah domin neman sauki a lokuta irin wannan."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
'Ba na dauke da coronavirus'

Asalin hoton, Getty Images
A wani taron manema labarai da ya gudanar jiya Juma'a a fadar White House, Donald Trump ya ce ba ya nuna wasu alamun kamuwa da kwayar cutar coronavirus.
Yana wannan magana ne bayan ganawa da ya yi da wani hadimin shugaban kasar Brazil.
"Ba ma dauke da alamar (kwayar cutar) ko kadan," ya fada yayin da yake amsa tambayar wata 'yar jarida.
Trump ya zauna kusa da shugaban Brazil Jair Bolsonaro a lokacin da suka ci abincin dare.
Wasu rahotanni sun ce Bolsonaro ya kamu da cutar amma shugaban ya musanta a jiya Juma'a. Sai dai an gano mai magana da yawunsa yana dauke da cutar.