Malamai sun ba da fatawar Sallar Juma'a kan coronavirus

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar manyan malaman addinin Musulunci ta bayar da wata fatawa, cewa an haramta wa mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus halartar sallar Juma'a da sauran sallolin jam'i a masallatai.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya rawaito cewa an gudanar da taro na 24 na majalisar ce a ranar Laraba don tattauna batun ko ya halatta ko bai halatta ba a halarci sallar Jumma'a da sauran sallolin jam'i a masallatai.
Majalisar ta kuma yanke shawara cewa, idan har hukumomin da aka dora wa alhakin aiwatar da matakan killace masu alaka da cutar Coronavirus suka bukaci duk wani mutum ya dakata daga halartar sallar Jumma'a da sauran salloli a masallatai, wajibi ne ya bi wannan umarni.
A irin wannan hali, sai mutumin da abin ya shafa ya yi sallolinsa a gida ko wurin da aka killace shi.
Malaman addinin Musuluncin sun kuma ce, idan wani yana tsoron kamuwa ko cutar da wasu, an halatta ya dakata da zuwa sallar Jumma'a da sallolin jam'i.
''Idan mutum bai halarci sallar Jumma'a ba a sakamakon wannan yanayi, sai ya yi sallar azahar mai raka'a hudu'', a cewar majalisar malaman.
Majalisar ta kuma yi kira ga illahirin al'ummar Musulmi da su bi umarni da ka'idojin da hukumomin da ke kula da lamarin cutar suka bayar.







