Dogarin David Cameron ya manta bindiga a bandakin jirgi

Asalin hoton, Getty Images
An fara bincikar dogarin tsohon firai ministan Birtaniya David Cameron sakamakon manta bindigarsa a bandakin jirgi.
Wani fasinjan jirgin ne ya ga bindigar lokacin da ya zagaya, a jirgin na kamfanin British Airways da ya taso daga New York don zuwa Landan a ranar Litinin.
Tuni aka tsare jami'in ake kuma aiwatar da bincike a kansa, kuma ofishin tsohon firai ministan ya ce ba zai ce komai dangane da lamarin ba.
Jami'in na aiki ne da sashen ba da kariya na rundunar 'yan sandan Birtaniya, kuma an ba da rahoton cewa ya cire rigarsa ne cancakat yayin da ya shiga makewayin.
An ga fasfon tsohon firai ministan da kuma na jami'in a kusa da bindigar da ya manta.
Wani mai magana da yawun 'yan sandan yankin ya ce ''Mun dauki wannan al'amari da muhimmanci, don haka muna yin bincike na cikin gida''.
Kamfanin jiragen saman na British Airways ya ce ya samar da wani tsari na musamman da jami'an 'yan sandan Birtaniya za su iya daukar makamai musamman bindiga a cikin jirgi, amma fa ya danganta da halin da ake ciki.
''Ma'aikatanmu sun shawo kan lamarin kafin jirgin ya tashi, don haka ba a samu wata matsala ba'', in ji kamfanin a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Mr Cameroon dai ya kasance firai ministan Birtaniya na tsawon sheakara shida har zuwa 2016, inda ya sauka saboda sakamakon zaben raba gardama da 'yan Birtaniya suka yi kan ficewar kasar daga Tarayyar Turai.











