Daya daga cikin manyan taurari na 'dab da yin bindiga'

Asalin hoton, ESA
Masana ilmin taurari a fadin duniya da suka hada da kwararru da ma wadanda ba kwararru ba sun zuba ido don jiran ganin daya daga cikin muhimman damarmaki a rayuwar duniya.
Ana tunanin cewa guda cikin taurarin da ke kan gaba wajen haska sararin samaniyar duniya da ake kira (Betelgeuse), na daf da gushewa dungurungun gabanin lokacin da aka yi hasashe tun da farko.
Hakan dai na nufin cewa tauraruwar za ta tarwatse.
Ko da yake da ma can masana sun yi hasashen faruwar hakan, sai dai a yanzu a iya cewa sabbin al'amura da suka faru a baya-bayan nan sun nuna akwai wata a kasa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a YouTube
Me ya sa masana ilimin taurari ke tunanin tauraruwar (Betelgeuse) za ta yi bindiga?
To a kashin gaskiya dai da ma an riga da an ayyana Betelgeuse a matsayin "tauraruwa mai wanzuwa" kana batun fashewarta al'amari ne na yaushe zai faru?
Ta shafe kusan shekaru miliyan takwas zuwa goma, idan aka kwatanta da shekaru biliyan hudu na rana, sai dai tana karar da makamashin rayuwarta cikin hanzari.
Tauraruwar dai jazazur take kuma a yanzu tana kusantar ajalinta.

Asalin hoton, ALMA
Sannan kuma ita wannan tauraruwa tana da girman gaske, takan kara girma sannan daga baya ta rika tsakurewa da kanta cikin buwayar Ubangiji, tana da jan hankali kwarai da gaske domin nisanta ya ninka daga inda muke zuwa wurin da rana take sau 550 zuwa 920, turkashi!
Daniel Brown, wani mataimakin farfesa ne a fannin ilimin sararin samaniya a Jami'ar Nottingham Trent, ya bayyana wa BBC cewa: "Tunanin da ake yi na tarwatsewarta na iya aukuwa daga nan zuwa kowanne lokaci.

Asalin hoton, Getty Images
A 'yan watannin da suka gabata masana ilimin taurari sun lura cewa (Betelgeuse) ta yi rauni sosai, masu bincike daga Jami'ar Villanova a Amurka sun yi ikirarin cewa a watan Disamba tauraruwar ta gama cin zamanancinta.
Halin da duniya ta tsinci kanta a ciki ya haifar da jita-jitar cewa babbar tauraruwar ta kusan gushewa.
Masana kimiyya sun yi ittifakin cewa asarar tauraruwar ba karamar asara ba ce musamman ta fuskar haska duniya.
Sarafina Nance, wata jami'ar kimiyyar sararin samaniya a California da ke nazari a kan (Betelgeuse), ta yi wani rubutu a shafinta na Twitter cewa "A yayin da babbar tauraruwa ke daf da gushewa to ya kamata a kwana da sanin muhimmancinta.

Asalin hoton, AFP
Emily Brundsen, wani masanin kimiyyar lissafi ne a Jami'ar York, ya gaya wa BBC cewa "ba mu taba samun damar sa ido kan yadda ayyukan tauraruwar ke gudana ba, don haka ko da yaushe akwai yuwuwar (fashewar ta kwatsam)''.
Me zai faru a yayin fashewar?
Fashewa ce mai tsoratarwa da kada hanta, kuma ko shakka babu zata amayar da makamashi mai dumbin yawan gaske.

Asalin hoton, Getty Images
Ba za ta gushe ba tare da an san da hakan ba.
"A 'yan kwanaki, Betelgeuse za ta zama mai haske kamar cikakken Wata," in ji Brown, daga bisani kuma sai ta kara gaba.
"Zai yuwu ta bayyana da tsakar rana."
Wannan tasiri na iya wuce tsawon watanni.
Tsaya tukunna, muna cikin hadari kenan?
Eh toh.. zancen dai shi ne idan tauraruwar ta fashe, hasken duniya na iya sauyawa baki daya.

Asalin hoton, NASA
Fashewar taurari a baya na da alaka da karuwar zafin yanayi, kana hakan na iya cutar da ƙwayoyin halittun da ke rayuwa a sararin samaniya.
Labari mai dadi shi ne cewa mu tamu ranar girmanta bai kai ta iya fashewa kamar Betelgeuse ba.
Sannan masana kimiyya na kallon Betelgeuse a matsayin tauraruwar da ba ta da hadari ga tamu duniyar.

Asalin hoton, Getty Images
"Betelgeuse na ba mu dama don lura da tsarin juyin halitta a cikin mutuwar wata tauraruwa da kuma ƙarin fahimta game da dunkulallun halittu ," in ji Emily Brundsen.
"Idan ta fashe a yanzu, zai zama mafarki mai ban tsoro ga duk masu ilimin sararin samaniya, kamar yadda ya zama dole mu sake tunani game da abin da muka sani game da taurari."
"Amma zai iya kasancewa abu mai kayatarwa."
Me yasa yake da wuya a san lokacin da zata fara gushewa?
Ko da yake an jima da adana bayanan "mutuwar taurari" da kuma tsarin gushewar su, sai dai ba a taɓa bibiyar lamarin sannu a hankali ba.

Asalin hoton, Getty Images











