Brexit: Abubuwa 7 da za su sauya bayan ficewar Birtaniya daga EU

Two people viewing Parliament with union jack umbrellas

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Tom Edgington
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

A ranar 31 ga watan Janairun 2020 ne Birtaniya za ta fice daga Kungiyar Tarayyar Turai a hukumance. Amma daga nan ne kasar take da tsawon wata 11 ta fice daga EU dungurungum.

Yayin da take cikin wannan yanayi kuma, Birtaniya za ta ci gaba da martaba dokokin EU da kuma biyan kudade ga EU.

Akasarin abubuwa za su kasance yadda suke amma za a samu wasu sauye-sauye:

1. 'Yan majalisar Turai daga Birtaniya za su rasa kujerunsu

Nigel Farage celebrating with newly-elected Brexit Party MEPS

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jam'iyyar Brexit ta lashe mafi yawan kujeru a zaben Turai da aka gudanar cikin Mayun 2019

Fitattun mutane irinsu Nigel Farage da Ann Widdecombe na daga cikin 'yan Birtaniya 73 da ke mambobi a majalisar Turai wadanda kai tsaye za su rasa kujerunsu a Majalisar Dokokin Turan.

Saboda a yanzu haka, Birtaniya za ta janye kanta daga dukkanin cibiyoyin siyasa da kuma hukumomin EU.

Sai dai kari kan bin dokokin EU da Birtaniya za ta ci gaba da yi a lokacin da take cikin shirin ficewa daga EU baki daya, kotun Tarayyar Turai za ta ci gaba da zama kan gaba wajen fadin abin da ya kamata a yi game da duk wata takaddama ta shari'a.

2. Babu sauran tarukan EU

Nan gaba zai kasance sai an gayyaci Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson idan har yana son shiga jerin sauran shugabanni don halartar tarukan majalisar EU.

Kazalika, ministocin Birtaniya su ma ba za su rika halartar tarukan da EU ke gudanarwa akai-akai ba wadanda ke yanke hukunci kan abubuwa da dama.

3. Za a rika jin abubuwa da dama game da kasuwanci

Birtaniya za ta samu damar tuntubar kasashe a fadin duniya game da gindaya wasu ka'idojin saye da sayarwa da kuma ayyuka.

Ba a ba ta izinin tattaunawar kasuwanci da kasashe irin su Amurka da Australiya a hukumance ba yayin da take zama mamba a EU.

Magoya bayan Brexit sun bayar da hujjar cewa samun 'yanci don kafa tsarin kasuwanci na kashin kai zai bunkasa tattalin arzikin Birtaniya.

Hakanan akwai abubuwa da yawa da za a tattauna tare da EU. Yarda da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Burtaniya da EU abu ne mai mahimmancin gaske, don haka ba a bukatar koma baya a fannin kasuwanci idan wa'adin ficewar ya kare.

Idan aka cimma yarjejeniya ta kasuwanci, ba za su iya farawa ba har sai lokacin da ficewar ta Birtaniya daga EU ta tabbata.

4. Za a ga sauyin launi a Fasfo din Birtaniya

British passports
Bayanan hoto, An koma yin amfani da sabon fasfo a 1988 sabanin mai launin shudi da aka yi amfani da shi a shekarun baya

Za a dawo yin amfani da fasfo mai launin shudi sama da shekara 30 bayan da aka daina yin amfani da shi, tare da maye gurbinsa da fasfo din da a yanzu ake amfani da shi mai launin makuba (burgundy).

Da yake sanar da sauyin a 2017, ministan shige da fice na lokacin, Brandon Lewis ya yaba da matakin komawa fasfo mai launin shudi da zinare mai dinbim tarihi wanda aka fara amfani da shi a 1921.

Za a fara bayar da sabon fasfo din nan da tsakiyar shekarar nan.

Kuma za a cigaba da yin amfani da fasfo din da ake amfani da shi yanzu

5. Tsabar kudin Brexit

Sajid Javid with the new coin

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Sai dai aka sake narka kwandalolin bayan da aka tsawaita ficewar Birtaniya daga EU

Za a fara amfani da kimanin miliyan uku na tsabar kudin 50 pence da ke dauke da kwanan watan "31 ga Janairu da kuma rubutun: "Zaman lafiya da wadata da abota da dukkan kasashe" ranar Juma'a.

Yin amfani da kwandalar ya janyo ce-ce ku ce inda wasu ke cewa ba za su goyi baya ba.

Gwamnati ta tsara za ta bijiro da makamancin tsabar kudin ranar 31 ga watan Oktoba, ranar da a baya aka tsara ficewar Birtaniya daga EU.

Sai dai an narka kwandalolin bayan da aka kara tsawaita Brexit.

6. Za a rufe sashen da ke tattauna ficewar Birtaniya daga EU

Za a rushe tawagar da ke kula da tattaunawar Birtaniya da EU ranar Brexit.

Tsohuwar Farai Minista Theresa May ce ta kafa sashen tattauna ficewar Birtaniya daga EU a shekarar 2016.

A tattaunawar da za a yi a nan gaba, tawagar za ta kasance a Downing Street.

7. Jamus ba za ta mayar da 'yan kasarta zuwa Birtaniya ba

Ba zai yiwu a mayar do da wasu da ake zargi da aikata laifi ba zuwa Birtaniya idan sun gudu zuwa Jamus.

Kundin tsarin mulkin Jamus bai yarda a fitar da 'yan kasar ba, sai dai in zuwa wata kasar ta Turai ce.

"Ba za a ci gaba da yin amfani da haka ba bayan Birtaniya ta bar EU," in ji wani mai magana da yawun Ma'aikatar Shari'a ta Jamus.

Babu tabbaci ko irin wannan takunkumin zai shafi wasu kasashe. Misali Slovenia, ta ce lamarin yana da rikitarwa, yayin da Hukumar Turai ta gaza yin jawabi a kai.

Ofishin Cikin Gida na Birtaniya ya ce za a ci gaba da amfani da izinin kame a yankin Turai a lokacin da Birtaniya ke shirin barin EU. (Wannan na nufin Jamus za ta iya mayar da mutanen da ba 'yan kasarta ba kasashensu.)

Amma, ofishin ya kara da cewa idan dokokin kasa suka hana mayar da mai laifi Birtaniya, "to ana tsammanin ofishin zai karbi ragamar shari'a ko hukuncin da aka yanke wa mutumin da abin ya shafa."

Abubuwa bakwai da ba za su sauya ba.......

Saboda da zarar Birtaniya ta fice daga EU, tana da tsawon wata 11 ta fice daga kungiyar baki daya kuma akasarin abubuwa za su kasance a yadda suke - har zuwa 31 ga watan Disambar 2020, ciki har da:

1. Tafiye-tafiye

People at an airport walking under a sign saying "arrivals from the European Union".

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a ci gaba da martaba 'yan Birtaniya kamar yadda ake yi wa sauran al'ummar EU a lokacin da kasar ke shirin ficewa daga EU

Jiragen sama da jiragen ruwa da kuma jiragen kasa za su ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Game da batun fasfo kuma, a lokacin da Birtaniya ke shirin ficewar, 'yan kasar za su ci gaba da samun damar bin layi a wuraren da aka kebe domin al'ummar da ke shiga Turai kadai.

2. Lasisin tuki da fasfo na dabbobin gida

Lasisin da fasfo din za su ci gaba da aiki matukar wa'adinsu bai kare ba.

3. Katin inshorar lafiya na Turai (EHIC)

A hand holding a European Health Insurance Card

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto, Za a ci gaba da yin amfani da katin EHIC

Wadannan su ne katunan da suke bai wa 'yan Birtaniya damar zuwa asibitocin gwamnati domin samun kulawa a lokacin rashin lafiya.

Ana iya amfani da su a kowace kasa ta EU (har ma da Switzerland da Norway da Iceland da kuma Liechtenstein) kuma za a ci gaba da amfani da su a lokacin barin EU gaba daya.

4. Zama da aiki a Turai

'Yan Birtaniya za su ci gaba da samun ikon zirga-zirga a lokacin shirin ficewar daga EU dungurungum don haka 'yan kasar ta Birtaniya za su ci gaba da zama tare da yin aiki a kasashen Tarayyar Turai kamar yadda suke yi a yanzu.

Haka abin yake ga 'yan kasashen Turai da ke son zama tare da yin aiki a Birtaniya ba.

5. Fansho

'Yan Birtaniya da ke zaune a Turai za su ci gaba da karbar fanshonsu sannan za su rika samun kari a kan kudaden fansho din duk shekara.

6. Bayar da gudunmowa a kasafin kudi

Birtaniya za ta ci gaba da biyan wani kaso a kasafin Turai yayin da take cikin wata 11 na shirin ficewarta daga EU din.

Hakan na nufin tsare-tsaren da ake da su wanda ake biya ta tallafin da EU ke bayarwa, ba za su fuskanci wani sauyi ba.

7. Kasuwanci

Kasuwanci tsakanin Birtaniya da EU zai dore ba tare da karin haraji ba.