Shugabannin G5 Sahel za su yi taro kan tsaro a Faransa

Emmanuel Macron da Mahammdou Issofou

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron zai karbi bakuncin takwarorinsa na yankin Sahel da ke yammacin Afirka, ranar Litinin domin tattaunawa game da yakin da sojoji suke yi da masu tada kayar baya.

Shugabannin Chadi da Nijar da Mali da Burkina Faso da Mauritania da ake kira G5 Sahel za su taru a kudancin birnin Pau na Faransa domin gudanar da taron.

Birnin Pau dai gida ne ga dakarun da ke yakar 'yan ta'adda karkashin shirin Operation Barkhane.

Shirin na fuskantar suka daga bangarori da dama saboda karuwar hare-haren masu tada tarzoma.

Ko a makon da ya gabata ma, sojoji 89 daga Nijar sun mutu a wani hari na baya-bayan nan da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji da dama.

Faransa ita ma ta rasa sojojinta 13 sakamakon wani harin jirgi mai saukar ungulu a Mali cikin watan Nuwamba.

Wani hari da aka kai a watan Disamba a Nijar ya zaburar da shugabannin yankin Sahel wajen yin kira ga kasashen duniya da su ba su tallafi a yakin da suke yi da masu ikirarin jihadi.