Kisan ma'aikatan agaji: MDD ta yi tir da Boko Haram

Ma'aikatan agaji na kungiyar Action Against Hunger da Boko Haram ta yi garkuwa da su

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yanzu Grace Taku ce ta rage a raye cikin ma'aikatan agajin, amma kungiyar Boko Haram ta ayyana ta a matsayin baiwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kisan ma'aikatan agaji da kungiyar Boko Haram ta yi a Najeriya.

A ranar Juma'a ce reshen ISWAP na kungiyar Boko Haram ta fitar da wani bidiyo mai tayar da hankali da ke nuna yadda mayakan kungiyar suka kashe ma'aikata hudu na kungiyar agaji ta Action Against Hunger.

Kisan ma'aikatan na zuwa ne kwana biyu bayan kashe sojoji 71 na Jamhuriyar Njiar mai makwabtaka da Najeriya da wasu mahara suka yi a wani kwanton bauna da suka yi wa sansanin sojojin. Hakan ya tilasta wa shugaban kasar Muhamadou Issoufou, katse halartar taron kasashen Afirka a kasar Masar inda ya koma gida.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya na ayyukan agaji (UNICA) da Action Against Hunger da gwamantin Najeriya sun yi tir da aika-aikar da kungiyar ta yi wa ma'aikatan agajin. Sun kuma mika ta'aziya ga iyalan mamatan.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jaddada bukatar kawo karshen miyagun ayyukan 'yan da'addan, yana mai cewa wajibi ne a tashi tsaye domin gani karshen danyen aikinsu.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniyar da kuma Kungiyar agajin sun bukaci Boko Haram da ta gaggauta sakin Grace Taku, ma'aikaciyar agajin da ta rage a hannunsu, wanda kungiyar ke bayyanawa a matsayin 'baiwa'.

Grace Taku, ita ce ma'aikaciyar Action Against Hunger da kuniyar Boko Haram ta sa ta yi bayani a madadin abokan aikinta a cikin wani bidiyo, kwanaki kadan bayan kunigyar ta kama su.

A watan Yuli ne kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da ma'aikatan agajin a lokacin da suke rabon kayayyakin abinci da magunguna ga mutane masu tsananin bukata a yankin Damasak da ke karamar hukumar Mobbar, a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya.